Bisa gayyatar da aka aika, mataimakin shugaban kasar Sin, Han Zheng, ya halarci bikin rantsar da shugaban Amurka, Donald Trump, a ranar Litinin a birnin Washington D.C.
A yayin zamansa a Amurka, Han, wanda yake wakilin musamman na shugaban kasar Sin, Xi Jinping, ya gana da zababben mataimakin shugaban kasar Amurka, J.D. Vance, da wakilan ‘yan kasuwar Amurka, da shugaban kamfanin Tesla, Elon Musk, da shugaban cibiyar bincike a kan inganta manufofi da shugabanci mai zaman kanta ta Amurka, Emeritus John Thornton da sauransu. (Abdulrazaq Yahuza Jere)