A yau Litinin ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya fara ganawa da shugabannin kasashen Afirka da za su halarci taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka ko FOCAC na shekarar 2024, wanda aka shirya gudanarwa tsakanin ranekun 4 zuwa 6 ga watan Satumba a nan birnin Beijing.
A yayin da yake ganawa da takwaransa na Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa, shugabannin biyu sun bayyana daga matsayin huldar kasashen su zuwa cikakkiyar hadin gwiwa bisa matsayin koli daga dukkanin fannoni a sabon zamani. Kaza lika, bayan tattaunawar da suka gudanar, shugabannin biyu sun ganewa idanunsu sanya hannu kan takardun wasu yarjejeniyoyin hadin gwiwa masu nasaba da cin gajiyar tsarin tauraron dan adam na ba da jagorancin taswira na Beidou, da gina matsugunan jama’a, da alakar cinikayya, da samar da damar cinikayyar albarkatun gona, da musayar al’adun gargajiya da sauran su.
- CMG Ya Watsa Shirin Talabijin Na Labaran Gaskiya Mai Taken “Abokai Na Kusa Daga Dukkanin Nahiyoyi”
- Masanin Habasha: Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Ya Jure Sauye Sauye Cikin Tsawon Lokaci
Sannan shugaba Xi ya gana da shugaban Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo Felix Tshisekedi, da shugaban kasar Mali Assimi Goita inda suka bayyana hadin gwiwasu wajen daukaka huldarsu zuwa abokantaka bisa manyan tsare-tsare.
Bugu da kari, shugaba Xi Jinping ya kuma gana da shugaban kasar Comoro Azali Assoumani, da shugaban kasar Togo Faure Gnassingbe, da shugaban kasar Djibouti Ismail Omar Guelleh, da shugabannin kasashen Guinea, da Eritrea, da Seychellesa daya bayan daya a nan Beijing.
Kazalika, Xi zai halarci bikin bude taron na FOCAC, tare da gabatar da muhimmin jawabi a ranar 5 ga watan Satumba, kuma zai shirya liyafar maraba ga shugabanni da wakilan da suka halarci taron. (Masu fassarawa: Saminu Alhassan, Mohammed Yahaya)