Shugaban kasar Sin kuma babban sakataren kwamitin koli na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping ya halarci bikin nune-nune mai taken “Yin kokari a sabon zamani” a dakin nune-nune na Beijing a yau.
Shugaba Xi ya jaddada cewa, bayan da aka gudanar da babban taron wakilan jam’iyyar Kwaminis ta Sin karo na 18, jam’iyyar ta jagoranci dukkan jama’ar kasar Sin daga kabilu daban daban, da daidaita matsalolin da aka gaza daidaita cikin dogon lokaci, kana an gudanar da manyan ayyukan tinkarar kalubale a fannonin siyasa, da tattalin arziki, da tsarin kasa, da yanayin halittu da sauransu.
Nasarorin da jam’iyyar Kwaminis ta Sin da kasar Sin suka samu sun aza tubalin cimma burin samun farfadowar al’ummar kasar Sin a fannonin tsarin kasa, da dukiya, da kuma tunani.
Ya ce ya kamata a yada matakai da ayyuka da nasarorin da aka samu a cikin shekaru 10 da suka gabata, da kuma tunani da ma’anar dake cikin tarihin jam’iyyar Kwaminis ta Sin, da sabuwar kasar Sin, da bude kofa ga kasashen waje da yin kwaskwarima a gida, da bunkasuwar tsarin gurguzu, da bunkasuwar al’ummar kasar Sin, yana mai cewa, ta hakan za a sa kaimi ga dukkan jama’ar kasar Sin wajen kara imani da jam’iyyar da kara kokari a nan gaba. (Zainab)