A yau Laraba 30 ga watan nan ofishin siyasa na kwamitin koli na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, ya gudanar da binciken gama-gari karo na 16, kan inganta aikin gina tsarin tsaro na zamani a kan iyakoki, da teku, da kuma sama.
Babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada a cikin wani muhimmin jawabi a yayin zaman nazarin cewa, inganta aikin gina tsarin tsaro a kan iyakoki, da teku, da kuma sama, wani muhimmin abu ne da ake bukata a zamanantar da tsaron kasa da soja. Ya ce yana da ma’anar da ta dace don tabbatar da samun ci gaba mai inganci bisa ga babban matakin tsaro, yana kuma da matukar muhimmanci a kai ga bunkasa aikin gina kasa mai karfi, da kuma farfado da al’umma ta hanyar zamanintarwa iri ta kasar Sin.
- An Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Hadin Gwiwa Tsakanin CMG Da AL
- Me Ya Kawo Matasa Zuwa Yankin Xizang Na Kasar Sin?
A cewarsa, kamata ya yi a fahimci sabon halin da ake ciki, da halayen musamman, da sabbin bukatun da ake da su kan tsaron iyakoki, da teku, da ma sama, da karfafa alhakin da ake dauka, da kaddamar da sabbin hanyoyi da matakai, da tabbatar da ayyuka bisa shirye-shiryen da aka yi, da nufin gina kakkarfan tsarin tsaro na zamani a kan iyakoki, da teku, da kuma sama.
An gudanar da wannan binciken gama-gari na ofishin siyasa na kwamitin koli na JKS ne a jajiberin ranar sojoji ta 1 ga watan Agusta. A madadin kwamitin koli na JKS da kwamitin aikin soja na tsakiya, Xi Jinping ya mika sakon taya murna ga dukkan sojojin’yantar da jama’a, da ’yan sanda masu dauke da makamai, da dakarun ko ta kwana. (Bilkisu Xin)