• English
  • Business News
Sunday, October 26, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Gwamnatin Jamus Friedrich Merz

by Sulaiman
5 months ago
Xi

LABARAI MASU NASABA

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

A yau Juma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tattauna ta wayar tarho da shugaban gwamnatin kasar Jamus Friedrich Merz, bisa gayyatarsa da aka yi.

Xi Jinping ya jaddada cewa, Sin da Jamus suna raya dangantakar dake tsakaninsu bisa girmama juna, da amincewa da bambance-bambance, da hadin gwiwa don samun moriyar juna, kuma akwai bukatar bangarorin biyu su yi kokari tare don tabbatar da raya dangantakarsu yadda ya kamata. Ya ce, da farko dai, ya kamata a yi imani da juna a fannin siyasa tsakanin kasashen biyu. Na biyu kuma, ya kamata a kara inganta dangantakarsu, wato ci gaba da hadin gwiwa a fannonin da suka riga sun hada hannu kamar su kera motoci, da injuna, da kuma masana’antar sinadarai da kuma kara fadada hadin gwiwarsu a sabbin fannoni kamar fasahar AI, da fasahar quantum da sauransu. Na uku kuma, ya kamata a kara karfi wajen hadin gwiwarsu, watau Sin tana fatan kasar Jamus za ta kara samar da goyon baya da sauki da gabatar da manufofi don inganta zuba jari da hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, ta yadda za a samar da yanayin cinikayya mai adalci da daidaito da gudanar da komai a bude, ga kamfanonin kasar Sin.

A nasa bangare, Merz ya bayyana cewa, sabuwar gwamnatin kasar Jamus za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka kan manufar Sin daya tak a duniya, da kokarin raya dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasashen biyu bisa halin da ake ciki yadda ya kamata. Har ila yau, ya ce kasar Jamus tana begen kara mu’amala da hadin gwiwa da kasar Sin, da bude kofarta ga kasashen waje da samun moriyar juna, da sa kaimi ga yin ciniki cikin adalci, da tabbatar da zaman lafiya a duniya, da kuma tinkarar kalubalen duniya kamar sauyin yanayi tare. (Zainab Zhang)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

October 25, 2025
Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur
Daga Birnin Sin

Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

October 25, 2025
Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki
Daga Birnin Sin

Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki

October 25, 2025
Next Post
Ko Kwamitin Saraki Zai Iya Ceto PDP Daga Rikicin Cikin Gida?

Ko Kwamitin Saraki Zai Iya Ceto PDP Daga Rikicin Cikin Gida?

LABARAI MASU NASABA

‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi

‘Yansanda Sun Kama Wasu Mutum Biyu Da Ake Zargi Da Haɗa Baki Da ‘Yan Bindiga A Kano

October 26, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwamnatin Kaduna Tare Da  AUDA–NEPAD Sun Tallafa Wa Manoma 400 Da Kayan Noma

October 26, 2025
Tornadoes Ta Doke Pillars A Wasan Farko Na Babaganaru

Tornadoes Ta Doke Pillars A Wasan Farko Na Babaganaru

October 26, 2025
Gwarzon Kamfanin Samar Da Kayayyakin Gida Na Mai Da Gas Na Shekarar 2025 Kamfanin GEIL

Gwarzon Kamfanin Samar Da Kayayyakin Gida Na Mai Da Gas Na Shekarar 2025 Kamfanin GEIL

October 26, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ɗan Majalisa Na Shekarar 2025: Benjamin Okezie Kalu

October 26, 2025
An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

October 25, 2025

Nafisa Abdullahi Aminu: Yarinyar Da Ta Ɗaukaka Darajar Nijeriya A Idon Duniya

October 25, 2025
Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Banki Na Shekarar 2025 Bankin Providus

October 25, 2025
Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki

Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki

October 25, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.