Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon taya murna ga taron koli na farko na manyan jami’an dandalin tattaunawa kan samun ci gaba tare na kasa da kasa, inda ya yi nuni da cewa, a halin yanzu ana fuskantar manyan sauye-sauye a fadin duniya, kuma an fuskanci matsaloli da dama yayin farfado da tattalin arzikin duniya, haka kuma ajandar ci gaban duniya tana fuskantar kalubale. Don haka ya gabatar da shawarar raya duniya, ta yadda za a gaggauta aiwatar da ajandar samun ci gaba mai dorewa ta MDD nan da shekarar 2030, da kara karfafa hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa, ta yadda za a samun ci gaba tare.
Xi ya ce, yana farin cikin ganin an samu sakamako a mataki na farko a bangaren hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa bisa shawarar, kuma kasashe masu tasowa da dama sun ci gajiyar hakan.
Shugaba Xi ya jaddada cewa, kasar Sin za ta kara zuba jari a fannin hadin gwiwar kasa da kasa, da yin aikin tare da sauran kasashen duniya domin taka rawa wajen tabbatar da ajandar samun ci gaba mai dorewa ta MDD nan da shekarar 2030 da gina al’umma mai kyakkyawar makomar bai daya ga daukacin bil Adama. (Mai fassara: Jamila)