Lahadin nan ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da wasikar taya murna ga bikin cika shekaru 100 da kafa kungiyar kula da nakasassu ta duniya (RI)
Shugaba Xi ya mika gaisuwa ga masu bukata ta musamman, ‘yan uwansu da ma’aikatan da suke yi musu hidima, ya kuma nuna godiyarsa ga kungiyoyin kasa da kasa da jama’a daga dukkan sassa da ke kula da kuma tallafawa harkokin nakasassu a kasar Sin.
Ya bayyana cewa, kasar Sin, tana ba da goyon bayan da ya dace ga aikin kula da masu bukata ta musamman, da daukar matakai na zahiri, don sa kaimi ga bunkasuwar harkokin nakasassu a kasashe masu tasowa, da sa kaimi ga al’ummomin kasa da kasa da su mai da hankali a kan nakasassu, da ba da gudummawa ga harkokin masu bukata ta musamman na kasa da kasa.
Xi ya bayyana cewa, kasar Sin tana kula da ma mai da hankali matuka kan masu bukata ta musamman, kuma za ta kara kyautata tsarin tsaron zamantakewa da ba da hidima ga nakasassu a cikin tsarin zamanantar da kasar, da sa kaimi ga ci gabansu.
An yau ne ake bikin cika shekaru 100 da kafa kungiyar kula da nakasassu ta kasa da kasa, kana ranar taimakon nakasassu ta kasar Sin a nan birnin Beijing.(Ibrahim)