A yau Asabar ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da wasikar taya murna ga taron fahimtar kasar Sin da ya gudana a birnin Guangzhou, da ke lardin Guangdong na kudancin kasar Sin.
A yayin da farfadowar duniya ke fuskantar rauni da kuma tashe-tashen hankula daga sassan duniya, dan Adam ya tsinci kansa a tsaka mai wuya a tarihi. Xi ya ce, abu ne mai matukar muhimmanci kasashen duniya su hada kai don tinkarar kalubaloli daban-daban na duniya, da inganta ci gaba tare, da kyautata jin dadin bil’Adama.
- Wakilin Sin Ya Yi Tir Da Matakan Matsin Lamba Da Nufin Dakile Tsarin Jagoranci Da Ci Gaban Duniya
- Basirar Henry Kissinger Abu Mai Daraja Ne Ga Amurka
“Don fahimtar kasar Sin, muhimmin abu shi ne fahimtar zamanantar da kasar Sin, kasar Sin tana ciyar da kyakkyawar manufar gina kasa mai girma da kuma farfado da al’umma daga dukkan bangarori ta hanyar zamananatarwa irin ta kasar Sin, da sa kaimi ga gina al’umma mai kyakkyawar maMataimakin firaministan kasar Sin Ding Xuexiang ya bayyana a jiya Jumma’a cewa, a matsayin babbar kasa mai tasowa mai sanin ya kamata, kasar Sin a shirye take ta yi aiki da dukkan bangarori domin gina duniya mai tsafta da kyau.
Ding, wakilin shugaban kasar Sin Xi Jinping na musamman, kuma zaunannen mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, ya bayyana hakan a lokacin da yake jawabi a wajen taron kolin kula da yanayi na duniya a birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).
Ding ya mika fatan alherin shugaba Xi ga UAE na karbar bakuncin taron. Ya ce, shekaru takwas da suka gabata, Xi ya yi aiki tare da shugabannin wasu kasashen duniya wajen cimma yarjejeniyar Paris tare da azama da hikimar siyasa, kuma ya fara wata sabuwar tafiya ta hadin gwiwa a duniya don magance sauyin yanayi.
A ko da yaushe kasar Sin tana kiyaye alkawuran da ta dauka, kuma tana ba da muhimmiyar gudummawa ga harkokin jagorancin duniya, a cewar Ding, ya kara da cewa, kasar Sin ta sa kaimi ga hadin gwiwar kasa da kasa kan harkokin kiyaye muhalli, da juyin juya halin makamashi, da sauyin yanayi, tare da tallafawa kasashe masu tasowa wajen kara karfinsu na tinkarar sauyin yanayi. (Mai fassara: Yahaya)koma ga bil’Adama,” a cewar Xi. “Makomar kasar Sin tana da nasaba sosai da makomar bil’Adama baki daya.”
Ya kara da cewa, kasar Sin na neman bunkasuwa mai inganci ta hanyar bude kofa ga kasashen waje, kana kasar Sin za ta ci gaba da samar da tsarin kasuwanci mai inganci, da tsarin kasuwancin duniya mai inganci bisa nagartaccen tsarin doka, kana za ta ci gaba da fadada bude kofa ga hukumomi dangane da dokoki da ka’idoji da daidaitattun tsarin gudanarwa. (Yahaya)