Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya amsa wasikar da wakilan tsofaffin daliban kasar Kenya na jami’ar Beijing Jiaotong suka rubuta masa, inda ya karfafa musu gwiwa da su ci gaba da ba da gudummawa wajen sada zumunta tsakanin kasashen Sin da Kenya da kuma tsakanin Sin da Afirka.
Xi ya yi nuni da cewa, shawarar ziri daya da hanya daya, ta gaskata manufar raya kasa da farfado da kasashen Sin da Kenya, tare da dunkule zaman lafiyar jama’ar kasashen biyu. Layin dogo tsakanin biranen Mombasa da Nairobi, wani muhimmin aiki ne kuma wani misali, mai nasara na hadin gwiwa tsakanin Sin da Kenya. Shugaba Xi ya ce, “Kun shaida kuma kun amfana da zumunci da hadin gwiwa tsakanin Sin da Kenya da kuma tsakanin Sin da Afirka, kuma kun ba da gudummawa tare da yada zumunci da hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka.”
A ‘yan kwanakin da suka gabata ne, tsofaffin daliban jami’ar Beijing Jiaotong ‘yan kasar Kenya, suka rubuta wa Xi wasika cewa, sun yi matukar farin ciki da zuwa kasar Sin don koyon aikin layin dogo, da sanin yadda ake tafiyar da harkokin sufurin jiragen kasa, kuma suna fatan za su ba da gudummawa wajen inganta zumunci da hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu, da bunkasa gina al’umma mai makomar bai daya ga daukacin bil-Adama. (Mai fassara: Ibrahim)