Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bukaci a gudanar da cikakken bincike tare da ceto mutanen da suka bace ko kuma suka makale a sanadiyar ambaliyar ruwa da bala’o’in yanayi, a wani umarni da ya bayar kan aikin da ya shafi rigakafin ambaliyar ruwa da agajin bala’o’i.
Xi, wanda shi ne babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban rundunar sojojin kasar, ya bukaci a yi kokarin rage yawan asarar rayuka. (Mai fassara: Ibrahim)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp