Da yammacin yau Laraba ranar 24 ga wannan wata da misalin karfe uku da rabi, gobara ta tashi a wani kanti dake gefen titin yankin Yushui na birnin Xinyu dake lardin Jiangxi na kasar. Kawo yanzu mutane 39 ne suka rasa rayukansu, wasu 9 kuma suka ji rauni, yayin da wasu mutane na makale a cikin ginin.
Bayan aukuwar hadarin, babban sakataren JKS kuma shugaban kasar Xi Jinping ya mai da hankali matuka kan lamarin, kuma ya ba da muhimmin umurni, inda ya bukaci a yi kokarin ceton mutanen da lamarin ya shafa, da kwantar da hankalin iyalan wadanda suka mutu. A sa’i daya kuma, a gudanar da bincike kan musabbabin aukuwar hadarin, domin hukunta wadanda abin ya shafa bisa doka.
Haka kuma Xi Jinping ya jaddada cewa, dole ne mu yi tsayin daka wajen dakile afkuwar hadurra iri-iri da kuma tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a da zaman lafiyar al’umma baki daya. (Mai fassara: Jamila)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp