Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci a kara kaimi ga horar da sojoji, da inganta daura damara da kara karfin ayyukan sojin sama, domin gina rundunar sojin sama mai karfi kuma na zamani.
Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kwamitin kolin sojan kasar, ya bayyana hakan ne a jiya Litinin a lokacin da ya ziyarci wasu dakarun sojan sama a birnin Xiaogan na lardin Hubei na kasar Sin. (Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp