A yau Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da jawabin bude taron kasa da kasa na Wuzhen kan kafar intanet.
Cikin jawabin da ya gabatar ta kafar bidiyo, Xi Jinping ya jaddada bukatar kasa da kasa su zurfafa musaya da hadin gwiwa a aikace, domin daukaka gina al’umma mai makoma ta bai daya a bangaren kafar intanet, zuwa wani sabon mataki.
- Darajar Cinikayyar Kasar Sin A Ketare Ya Karu Da Kaso 0.03% Cikin Watanni 10 Na Bana
- Kalaman Amurka Zai Iya Shafar Tattalin Arzikin Nijeriya – Minista
Ya kara da kira da a ba da fifiko ga samar da ci gaban kafar intanet domin karin kasashe da jama’ar duniya su ci gajiyarsa.
Yayin da yake kira da a samar da kafar intanet mai karin tsaro da aminci, ya ce akwai bukatar girmama ‘yancin da kasashe ke da shi kan kafarsu ta intanet da kuma yadda ko wace kasa ke son tafiyar da harkokin bangaren. Haka kuma, a yi adawa da masu neman babakere da fito-na-fito da gasar mallakar makamai a kafar intanet. (Fa’iza Mustapha)