Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci liyafar cin abincin dare da aka shirya masa Laraba agogon wurin a birnin San Francisco na Amurka, kuma ya gabatar da wani jawabi, inda ya bayyana cewa, kasar Sin a shirye take ta gayyaci Amurkawa matasa 50,000 zuwa kasar Sin kan shiriye-shirye na musaya da karatu a cikin shekaru 5 masu zuwa don kara karfafa mu’amala tsakanin al’ummomin kasashen biyu, musamman a tsakanin matasa.
Xi ya ce, “Al’ummominmu ne suka shimfida ginshikin dangantakar Sin da Amurka”, yana mai jaddada cewa, “Jama’armu ce ta bude kofar huldar dake tsakanin Sin da Amurka, al’ummominmu ne suka rubuta labaran huldar dake Sin da Amurka, kuma jama’armu ne za su samar da makomar dangantakar sassan biyu.”
Ya kara da cewa, “Ya kamata mu kara gina gadoji da shimfida hanyoyi da dama domin mu’amala tsakanin jama’a. Bai kamata mu kafa shingaye ko haifar da sanyin gwiwa ba.”
A halin yanzu dai, shugaban na kasar Sin ya ce kofar dangantakar Sin da Amurka ba za ta sake rufewa ba da zarar an bude ta, kuma manufar abotar Sin da Amurka ba za ta kauce hanya tsaka da farawa ba. (Mai fassara: Yahaya)