ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, November 14, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Xi Ya Halarci Kwaya-Kwaryan Taron Shugabannin Mambobin APEC

by CMG Hausa
2 years ago
taro

Da tsakar ranar jiya agogon wurin ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci kwarya-kwaryar taron tattaunawa da kuma liyafar cin abincin rana tsakanin shugabannin mambobin kungiyar APEC da baki da suka karbi bakuncinsu a San Francisco na kasar Amurka.

A yayin taron, Xi Jinping ya nuna cewa, a ’yan shekarun baya-bayan nan, kungiyar APEC ta kara karfin tabbatar da manufofin Putrajaya nan da shekaru 2040, da kuma tabbatar da manufofin Bangkok na samun ci gaban tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba, ta yadda za a taka rawa a bangaren samun bunkasuwa a duniya ba tare da gurbata muhalli ba. A bisa halin da ake ciki yanzu, kamata ya yi, kasashe daban-daban su kai ga cimma matsaya daya da daukar mataki tare, don ba da gudunmawarsu a wannan fanni. Kan haka Xi Jinping ya ba da shawarwari guda uku:

Na farko, gaggauta tabbatar da ajandar samun ci gaba mai dorewa ta MDD nan da shekarar 2030. Kana Sin kuma ta gabatar da shawararin samun bunkasuwar duniya, wanda zai taka rawa wajen karawa kasashen duniya kwarin gwiwar hada kai don tinkarar gibin da ake samu ta fuskar ci gaban tattalin arziki.

ADVERTISEMENT

Na biyu, a fito da wata sabuwar hanyar samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba, ta yadda za a kafa wani yanayi mai adalci tsakanin bunkasuwar tattalin arziki da kiyaye muhalli.

Na uku, hadin kan kasashen duniya wajen tinkarar sauyin yanayi. Kiyaye yarjejeniyar MDD kan sauyin yanayi a matsayin babbar hanyar tafiyar da harkoki masu alaka da yanayin duniya. Da magance matsalolin da ke damun kasashe masu tasowa ta fuskar kudade, inganta kwarewa da musayar fasahohi, ta yadda za a tabbatar da yarjejeniyar tinkarar sauyin yanayi na MDD da ta Paris.

LABARAI MASU NASABA

Editoci Sun Yi Gargadi Kan Rushewar Kafofin Yada Labarai Sakamakon Matsin Tattalin Arziki

Kotu Ta Yanke Wa Mutum 4 Hukuncin Kisa Kan Kashe Wani Makanike A Kano

Ban da wannan kuma, Xi Jinping ya jaddada cewa, Sin tana kokarin tabbatar da shawarar “ziri daya da hanya daya” a bangare kiyaye muhalli, za kuma ta ci gaba da gina manyan ababen more rayuwa ba tare da gurbata muhalli ba, da samar da tsabtaccen makamashi da amfani da shi a fannin zirga-zirga. Sin na fatan hada kai da bangarori daban-daban don kara ba da gudunmawa wajen gina kyakkyawar makomar Bil Adama ta bai daya na samun bunkasuwa tare, da samar da yanayi mai kyau a duniya.

Shugaban kasar Amurka Joe Biden ne ya jagoranci wannan taro mai taken “Samun bunkasuwa mai dorewa da lura da sauyin yanayi da zamanintar da makamashi.”
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi shi ma ya halarci wannan taro.(Amina Xu)

  • Xi Ya Gabatar Da Jawabi Yayin Liyafar Da Aka Shirya Masa A San Francisco
ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Editoci Sun Yi Gargadi Kan Rushewar Kafofin Yada Labarai Sakamakon Matsin Tattalin Arziki
Labarai

Editoci Sun Yi Gargadi Kan Rushewar Kafofin Yada Labarai Sakamakon Matsin Tattalin Arziki

November 14, 2025
Kotu Ta Yanke Wa Mutum 4 Hukuncin Kisa Kan Kashe Wani Makanike A Kano
Manyan Labarai

Kotu Ta Yanke Wa Mutum 4 Hukuncin Kisa Kan Kashe Wani Makanike A Kano

November 14, 2025
Bayan Barazanar Amurka: Sultan Ya Nemi Hadin Kan ‘Yan Nijeriya Wajen Yaki Da Ta’addanci
Manyan Labarai

Bayan Barazanar Amurka: Sultan Ya Nemi Hadin Kan ‘Yan Nijeriya Wajen Yaki Da Ta’addanci

November 14, 2025
Next Post
San Francisco sabon mafarin hadin gwiwar Sin da Amurka ne

San Francisco sabon mafarin hadin gwiwar Sin da Amurka ne

LABARAI MASU NASABA

Masana’antu Masu Zaman Kansu A Arewa Sun Yi Maraba Da Harajin Kashi 15 Na Shigo Da Man Fetur

Masana’antu Masu Zaman Kansu A Arewa Sun Yi Maraba Da Harajin Kashi 15 Na Shigo Da Man Fetur

November 14, 2025
Ronaldo Na Fuskantar Dakatarwar Wasanni Biyu Bayan Samun Jan Kati

Ronaldo Na Fuskantar Dakatarwar Wasanni Biyu Bayan Samun Jan Kati

November 14, 2025
Editoci Sun Yi Gargadi Kan Rushewar Kafofin Yada Labarai Sakamakon Matsin Tattalin Arziki

Editoci Sun Yi Gargadi Kan Rushewar Kafofin Yada Labarai Sakamakon Matsin Tattalin Arziki

November 14, 2025
Kotu Ta Yanke Wa Mutum 4 Hukuncin Kisa Kan Kashe Wani Makanike A Kano

Kotu Ta Yanke Wa Mutum 4 Hukuncin Kisa Kan Kashe Wani Makanike A Kano

November 14, 2025
Abin Da Ya Sa NPA Ta Yi Hadaka Da ‘Snake Island Port’ -Dakta Dantsoho

Abin Da Ya Sa NPA Ta Yi Hadaka Da ‘Snake Island Port’ -Dakta Dantsoho

November 14, 2025
Shugaban NPA Ya Bukaci A Yi Hadaka Domin Cin Gajiyar Albarkatun Fannin Sufurin Afirka

Shugaban NPA Ya Bukaci A Yi Hadaka Domin Cin Gajiyar Albarkatun Fannin Sufurin Afirka

November 14, 2025
Bayan Barazanar Amurka: Sultan Ya Nemi Hadin Kan ‘Yan Nijeriya Wajen Yaki Da Ta’addanci

Bayan Barazanar Amurka: Sultan Ya Nemi Hadin Kan ‘Yan Nijeriya Wajen Yaki Da Ta’addanci

November 14, 2025
Jan Aikin Da Ke Gaban Manyan Hafsoshin Tsaron Nijeriya

Jan Aikin Da Ke Gaban Manyan Hafsoshin Tsaron Nijeriya

November 14, 2025
Sin: Ya Zama Wajibi Japan Ta Janye Kalamanta Dangane Da Taiwan 

Sin: Ya Zama Wajibi Japan Ta Janye Kalamanta Dangane Da Taiwan 

November 13, 2025
Li Qiang Zai Halarci Tarukan SCO Da G20 Tare Da Ziyarar Aiki A Zambia

Li Qiang Zai Halarci Tarukan SCO Da G20 Tare Da Ziyarar Aiki A Zambia

November 13, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.