A yau Talata ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jagoranci taro karo na uku na kwamitin kolin JKS, kan zurfafa yin gyare-gyare a kasar, inda aka yi nazari tare da amincewa da wasu muhimman takardu kamar “Ra’ayoyin inganta aikin gina kyakkyawar kasar Sin”, da “Ra’ayoyin ba da jagoranci kan karfafa tsarin kula da muhallin halittu”.
Yayin da yake jagorantar taron, shugaba Xi ya jaddada cewa, gina kyakkyawar kasar Sin wani muhimmin buri ne na gina kasa mai bin tsarin gurguzu ta zamani a dukkan fannoni, kuma ya zama wajibi a tabbatar da cewa, an cimma wannan buri nan da shekarar 2035. Don haka ya yi kira da a ci gaba da inganta matakan rigakafi da kandagarkin gurbatar muhalli, da hanzarta sauya matakan samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, inganta mabambanta tsarin muhalli, da raya ingantaccen yanayin muhalli. (Mai fassara: Ibrahim)