Babban sakataren kwamitin koli na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping a yau Litinin ya jaddada cewa, za a ci gaba da kiyaye shugabancin jam’iyyar gaba daya kan kungiyoyin kwadago, da kuma hada kan daruruwan miliyoyin ma’aikatan kasar don shiga babban aikin gina kasa mai karfi da farfado da kasar gadan-gadan.
Xi, wanda kuma shi ne shugaban kasar Sin, kuma shugaban kwamitin koli na soja na kasar, ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da sabbin shugabannin gamayyar kungiyoyin kwadago ta kasar Sin. (Yahaya)