Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira da a kara azamar gina kakkarfar rundunar soji ta zamani, mai ikon taimakawa da fasahohi da bayanan da ake bukata ta fannin fasahohin sadarwa, kana da cimma nasarar gaggauta samar da ci gaba, a fannin cin gajiya daga fasahohin sadarwa.
Shugaba Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin JKS, kuma shugaban hukumar zartarwa ta rundunar sojojin kasar Sin, ya yi wannan tsokaci ne a jiya Laraba, yayin da ya ziyarci rundunar sojin kasar Sin mai taimakawa a fannin fasahohin sadarwa. (Mai fassara: Saminu Alhassan)