A yau Alhamis, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon taya murna ga Netumbo Nandi-Ndaitwah, bisa nasarar da ta samu ta lashe zaben shugaban kasar Namibia.
Cikin sakon nasa, shugaba Xi ya ce Sin da Namibia na da dadadden tarihi na kawancen gargajiya, kuma a shekarun baya bayan nan, kasashen biyu sun karfafa amincewarsu ga juna ta fuskar siyasa, da cimma sakamako mai gamsarwa a fannin hadin gwiwa na zahiri.
Kaza lika a sakon nasa, Xi ya ce yana matukar dora muhimmanci ga bunkasar hadin gwiwar kasarsa da Namibia, kuma a shirye yake ya yi aiki tare da shugaba Nandi-Ndaitwah, wajen daga matsayin kawancen gargajiyar kasashen biyu, da zurfafa cimma moriyar hadin gwiwa, ta yadda hakan zai haifar da moriya ga al’ummun sassan biyu. (Mai fassara: Saminu Alhassan)