Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sha alwashin karfafa hadin gwiwa da shugaban jamhuriyar Congo Denis Sassou Nguesso, ta yadda sassan biyu za su kai ga daga matsayin hadin gwiwar su zuwa matsayin koli daga dukkanin fannoni.
Shugaba Xi ya bayyana hakan ne a Alhamis din nan, yayin da yake musayar sakon taya murnar cika shekaru 60, da kulla dangantakar hadin gwiwa tsakanin Sin da Congo tare da shugaba Sassou.
- Wakilin Sin: Kuri’ar Kin Amincewar Da Amurka Ta Jefa Kan Kudurin Tsagaita Wuta A Gaza Ta Rushe Matsayar Kwamitin Sulhun MDD
- Shugaban Faransa Ya Gana Da Wang Yi
Shugaban na Sin ya ce duk da sauye sauye a harkokin kasa da kasa, cikin shekaru sama da 60, Sin da Congo sun wanzar da hadin gwiwa, da bunkasa ci gaban juna, ta yadda kasashen biyu suka zamo abokai na hakika da suka amince da juna ta fuskar siyasa, kana sun zamo abokan cimma moriyar juna ta fannin hadin gwiwar raya tattalin arziki.
Xi ya kara da cewa, yana dora muhimmancin gaske ga bunkasar dangantakar sassa biyu, kuma a shirye yake ya yi aiki da shugaba Sassou, wajen mayar da wannan biki na cikar dangantakar su shekaru 60 wani mafari, na ci gaba da bunkasa alaka zuwa matsayin koli daga dukkanin fannoni.
A nasa bangare kuwa, shugaba Sassou cewa ya yi cikin shekarun 60, al’ummun kasar sa da na Sin sun dinke waje guda, sun raya burin bai daya na wanzar da zaman lafiya, da adalci da samun wadata. Wanda hakan ya ingiza ci gaban kasashen a dukkanin fannoni. (Mai fassara: Saminu Alhassan)