Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da wasikar taya murna ga jami’ar Tianjin wacce take bikin cika shekaru 130 da kafuwa.
Xi ya kuma mika sakon taya murnar ga malaman jami’ar, da dalibai masu karatu yanzu da kuma tsofaffin dalibanta.
A cikin wasikar ta mayar da amsa mai dauke da kwanan watan jiya Talata, Xi ya bayyana bikin a matsayin wani sabon lale ga jami’ar, ya kuma yi kira ga malaman jami’ar da dalibanta da su mai da hankali kan manyan bukatun kasa.
Ya bayyana fatansa na zurfafa yin gyare-gyare a fannin koyarwa da binciken kimiyya, da karfafa kwazon gudanar da bincike, da samun manyan sabbin nasarori a fannin kimiyya da fasaha.
Har ila yau, Xi ya bukace su da su inganta ci gaban hazaka, da karfafa bunkasar tattalin arziki da zamantakewa, da ba da gudummawa ga kokarin kasar na gina ingantaccen tsarin ilimi, da kara karfin kimiyya da fasaha, da zurfafa zamanantar da kasar Sin.
Jami’ar Tianjin wadda aka kafa a shekarar 1895 a matsayin jami’ar Peiyang, ita ce jami’ar zamani ta farko ta kasar Sin kuma ta yi na’am tare da amsa sunanta na yanzu ne a shekarar 1951. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp