A yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika sakon taya murna ga takwaransa na kasar Papua New Guinea Bob Dadae murnar cika shekaru 48 da samun ‘yancin kan kasar.
A cikin sakon nasa, shugaba Xi Jinping ya yi nuni da cewa, tun bayan da aka kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da Papua New Guinea, kasashen biyu na zurfafa mu’amala da hadin gwiwa a tsakaninsu a dukkan fannoni, hakan ya amfanawa jama’ar kasashen biyu. Ya bayyana cewa, Sin da Papua New Guinea dukkansu muhimman kasashe a yankin Asiya da tekun Pasifik, kana suna da ra’ayi daya wajen samun moriyar juna da yin hadin gwiwa a fannonin raya kasa da tabbatar da adalci a duniya. Kasar Sin tana dora muhimmanci sosai kan raya dangantakar dake tsakaninta da Papua New Guinea.
Ya ce, yana son yin aiki tare da shugaba Bob Dadae wajen sa kaimi ga inganta dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni a tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon mataki, da kuma amfanawa jama’ar kasashen biyu baki daya. (Zainab)