Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a yau Lahadi cewa, cikin shekaru 10 da suka gabata, an samu wasu manyan nasarori 3 masu matukar muhimmanci, wandada suka shiga tarihin JKS da al’ummar kasar.
Xi Jinping ya bayyana yayin bude babban taron mambobin JKS karo na 20 cewa, “Mun cika shekaru 100 da kafuwar JKS, gami da mun shiga wani sabon zamani na gurguzu mai sigar kasar Sin, kuma mun fatattaki kangin talauci baki daya, kana mun kammala ginin al’umma mai matsakaicin ci gaba ta kowanne bangare, wato dai, mun cika burinmu na farko a lokacin da muke murnar cika shekaru 100 da kafuwar JKS.”
A cewarsa, wadannan muhimman nasarori ne da suka shiga tarihi, nasarorin da JKS da al’ummar Sinawa suka yi namijin kokarin cimmawa cikin hadin kai, kuma nasarorin da za su kasance cikin tarihin kasar har abada, wadanda kuma za su yi gagarumin tasiri ga duniya.
Baya ga haka, shugaban kasar Xi Jinping ya yi kira ga dukkan mambobin JKS da su himmantu cikin hadin kai, wajen tabbatar da gina kasar Sin mai tsarin gurguzu ta zamani ta kowacce fuska.
Xi Jinping ya ce taron ya zo ne a lokaci mai muhimmanci, kasancewar jam’iyyar da daukacin Sinawa daga dukkan kabilu, na kan wata sabuwar hanya ta gina kasar zuwa ta zamani mai bin tsarin gurguzu ta kowacce fuska, da kuma kokarin cimma buri na biyu lokacin da za a yi murnar cika shekaru 100 da kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin.
Taken taron shi ne, daukaka tsarin gurguzu mai sigar kasar Sin da aiwatar da tunanin gurguzu mai sigar kasar Sin a sabon zamani da ci gaba da daukaka babban ruhin da jam’iyyar ta kafu a kai da kasancewa cikin kwarin gwiwa da karin karfi, da daukaka muhimman ka’idojin jam’iyyar da samun sabbin nasarori da ci gaba da tabbatar da karfi da kuzarinta da himmantuwa cikin hadin kai wajen gina kasa ta zamani mai bin tsarin gurguzu ta kowacce fuska, tare da kara farfado da kasar ta kowanne bangare.
Cikin rahoton da ya gabatar a yayin bikin bude babban taron, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya kuma ce JKS za ta aiwatar da dukkanin manuofi da za su ba da damar warware batun yankin Taiwan a sabon zamani, tare da tabbatar da cimma burin dinkewar sassan kasa.
Shugaba Xi ya ce warware batun Taiwan harka ce ta kasar Sin, wadda ya zama wajibi Sin din ta magance ta. Ya ce “Za mu ci gaba da yin aiki tukuru, domin warware wannan batu cikin lumana bisa gaskiya da kwazon aiki, amma ba za mu alkawarta kore yiwuwar amfani da karfi ba, kana muna da nufin duba yiwuwar daukar dukkanin matakai.
Ya kamata masu kokarin tsoma baki na waje, da kuma masu burin ballewar yankin Taiwan da dukkanin ayyukansu su san haka. Ban ambaci hakan domin ’yan uwan mu na Taiwan ba”.
Ban da wannan kuma, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana yayin bude taron mambobin JKS karo na 20 a yau Lahadi cewa, kasarsa ba za ta taba neman yi wa kasashen duniya babakere ko fadada iko da yankunanta ba.
A cewarsa, kasar Sin ta tsaya ne tsayin daka, wajen adawa da duk wani nau’i na babakere da neman iko da yakin cacar baka da tsoma baki cikin harkokin gidan kasashe da kuma nuna fuska biyu. (Masu fassara: Saminu Alhassan, Fa’iza Mustapha)