Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira da a kara kaimi ga shirin sanya sojojin kasar cikin shirin yaki, yayin da ya kai ziyarar aiki a rundunar da ke da hedkwata a yankin arewa maso gabashin kasar.
Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban kwamitin koli na soja, ya bayyana haka ne a lokacin da ya ziyarci runduna ta 78 a Juma’ar da ta gabata.
Shugaba Xi ya bukaci a yi kokarin inganta matakin shirye-shiryen yaki, da karfafa horar da muhimman fannoni da wadanda ke wahala, tare da tsara sabbin dabarun yaki.
Xi ya kuma jaddada muhimmancin karfafa gina jam’iyyar, da kiyaye mutunci da hadin kan sojojin kasar, da tabbatar da zaman lafiya da tsaronsu. (Ibrahim)