Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira da a kara kaimi wajen ciyar da aikin farfado da al’ummar kasar Sin gaba, da rubuta wani sabon babi na gina kasa mai bin tsarin gurguzu ta zamani daga dukkan fannoni.
Shugaba Xi ya bayyana haka ne, a yayin wani taron karawa juna sani da aka shiryawa jami’an larduna da ministoci, da aka gudanar daga jiya Talata zuwa Larabar nan a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, a shirye-shiryen gudanar da babban taron wakilan JKS karo na 20.
Xi ya jaddada cewa, zamanantarwa da muke fafatuka, shi ne zamanantar da kasa mai bin tsarin gurguzu karkashin jagorancin JKS. Tilas ne mu ci gaba da zage damtse, wajen farfado da al’ummar Sinawa ta hanyar zamanantarwa mai sigar kasar Sin.
Haka kuma, ba za mu bi tsohuwar rufaffiyar hanya mai tsauri ba, kuma ba za mu bi karkatacce tafarkin ba, za mu dora ci gaban kasa da al’umma bisa karfin kanmu, da martaba makomar ci gaban kasar Sin da nasarorin da ake samu a hannunmu.
Shugaba Xi ya kuma bayyana cewa, JKS, ita ce babbar jam’iyya mai mulki mai bin salon markisanci a duniya. Kuma don karfafa matsayinta na dogon lokaci da samun goyon bayan jama’a, wajibi ne a ko da yaushe ta kasance mai cikakken iko da tabbatar da shugabanci ga jam’iyyar. (Ibrahim)