Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga lardin Jiangxi dake yankin gabashin kasar, da ya yi amfani da karfinsa, da inganta rauninsa, don rubuta babinsa a kokarin da ake na zamanantar da kasar Sin.
Xi ya bayyana haka ne a yayin ziyarar da ya kai lardin daga ranar Talata 10 zuwa Jumma’ar nan 13 ga watan Oktoba.
Xi ya jaddada muhimmancin zurfin tunani da yin kokari da babu kamarsa. (Ibrahim)