Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga ‘yan kwadago dake aiki a masana’antu, da su ba da gudummawar cimma nasarar cikakken aikin farfado da yankin arewa maso gabashin kasar Sin.
Shugaban na Sin ya bukaci ‘yan kwadagon da su gabatar da gudummawar basirar su, da karfin su wajen gina kasa mai tasirin sarrafa hajoji, da yayata burin farfado da arewa maso gabashin kasar Sin.
Xi, ya yi kiran ne cikin martanin wasikar da wakilan ‘yan kwadago na wata babbar masana’antar samar da manyan kayayyakin aiki dake birnin Qiqihar na lardin Heilongjiang dake arewa maso gabashin kasar Sin suka aika masa. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp