Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ya sanar a yau Juma’a cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci taron kolin BRICS karo na 16 a birnin Kazan na kasar Rasha daga ranar 22 zuwa ta 24 ga watan Oktoba bisa gayyatar da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya yi masa.
Har ila yau ita ma mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta shaidawa manema labarai a wannan rana cewa, wannan taron da ke tafe, wanda shi ne na farko da za a yi bayan kara yawan mambobin BRICS, ya ja hankalin al’ummomin duniya baki daya.
- Gudunmawar Da Sin Take Bayarwa Wajen Tabbatar Da Wadatar Abinci A Duniya
- Yawan Karuwar GDPn Sin Daga Watan Janairu Zuwa Satumban Bana Ya Kai 4.8% Bisa Na Makamancin Lokacin A Bara
A cewar Mao, Xi zai halarci kanana da manyan tarukan shugabanni, da tattaunawar shugabannin BRICS Plus, da gabatar da muhimman jawabai. Kazalika, shugaba Xi zai yi mu’amala mai zurfi tare da shugabannin wasu kasashe kan halin da ake ciki a duniya, da hadin gwiwar kasashe mambobin BRICS a aikace, da bunkasa tsarin BRICS, da muhimman batutuwan da suka shafi moriyar kasashen.
Mao ta kara da cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da dukkan bangarori, domin tabbatar da ci gaba mai dorewa a hadin gwiwar BRICS, da bude wani sabon babi na hadin kai da inganta kai ga kasashe masu tasowa, da sa kaimi ga zaman lafiya da ci gaban duniya baki daya. (Yahaya)