Jiya da yamma ne Xu Guixiang, kakakin gwamnatin jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta ta kasar Sin ya nuna cewa, babu batun aikin tilas a masana’antar samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana a Xinjiang.
Xu ya fadi haka ne a yayin taron manema labaru da aka shirya dangane da jihar Xinjiang a birnin Beijing.
Dangane da kalaman da aka baza a duniya a kwanan baya dangane da masana’antar samar da wuta mai amfani da hasken rana a Xinjiang, Xu ya nuna cewa, dalilan da suka sa Xinjiang ta zama wurin dake karfin samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana, su ne na farko akwai hasken rana sosai a jihar, ga kuma bambancin fasaha, sa’ana nan an bar kasuwanni su yi halinsu.
Haka ya dace a bunkasar masana’antar samar da wuta mai amfani da hasken rana a duniya, da ma ci gaban sauran masana’antun kasa da kasa.
Ainihin muhimmin dalilin da ya sa tsarin masana’antar samar da wuta mai amfani da hasken rana na duniya yake da rauni shi ne, yadda kasar Amurka ta aiwatar da shirin dokar nan, wai ta hana yin aikin tilas ta Uygur, ta dakile ci gaban masana’antar samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana na kasar Sin.
Xu ya ce, “Mugun nufin Amurka, ya saba wa ka’idojin kasuwa da na kungiyar ciniki ta kasa da kasa wato WTO, kuma hakan ya illanta tsari da ka’idar cinikayyar kasa da kasa, kana ya kawo cikas ga hadin gwiwa da bunkasar masana’antar samar da wuta mai amfani da hasken rana a duniya, ta kuma yi barna ga tsarin masana’antar.
Barnar da ta haddasa, za ta yi illa matuka ga masana’antar a duniya, kuma tabbas za ta yi illa ga moriyar kamfanonin Amurka. Abin da Amurka ta aikata, zai yi mata illa da ma sauran kasashe.” (Tasallah Yuan)