Gwamna Dauda Lawal ya tabbatar wa rundunar sojojin ƙasar nan jajircewar gwamnatinsa wajen bai wa jami’an soji cikakken goyon bayan gwamnatin sa a jihar Zamfara.
Ranar Juma’ar da ta gabata, Gwamna Lawal ya karɓi baƙuncin Babban Hafsan tsaron ƙasa (CDS), Janar Christopher Gwabin Musa a tsohon ɗakin taron fadar gidan gwamnati da ke Gusau.
- Gwamnatin Zamfara Ta Tabbatar Da Mutuwar Mutane 40 A Hatsarin Kwale-kwale
- Bukukuwan Mauludi: Wani Mummunan Hatsari Ya Ci Rayukan Mutane 40 A Saminaka
Sanarwa daga mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ta bayyana cewa Babban Hafsan tsaron ya sanar da wani laƙabi da za a rinƙa kiran rundunar haɗin gwiwa ta yaƙi da ta’addanci a yankin Arewa maso Yamma, inda ya ce za a rinƙa kiranta da ‘rundunar samamen Fansan Yamma, wanda kuma yanzu ita ce rundunar da aka sani a yankin Arewa maso Yamma.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, wannan runduna ta ‘Operation Fansan Yamma,’ wani laƙabi ne da ke nuni da cewa jami’an tsaron a shirye su ke don ganin sun murƙushe harkar ‘yan bindiga a yankin na Arewa maso Yamma.
Cikin jawabin sa, Gwamna Dauda ya yaba wa Babban Hafsan bisa irin namijin ƙoƙarin da ya ke yi wajen magance matsalolin tsaro a ƙasar nan.
“Janar, kasancewarka a Zamfara a wannan lokaci, ya ƙara ƙara wa jami’an soji ƙwarin gwiwa. Ka ƙara tabbatar da fatan mu, al’umma na cike da fata.
“Ba za mu taɓa yin wasa da wannan ziyara ba. Gwamnatina ta jajirce wajen haɗa kai da Hukumomin tsaro don tabbatar da tsaro a jihar Zamfara.
“Bisa la’akari da jawabinka, ina da tabbacin cewa zaman lafiya zai dawo a Zamfara. Ka yi makaranta a nan, ka san irin yanayin zaman lafiyar da ake da shi a da. Gusau ta kasance birni na biyu a harkar Kasuwanci a Arewa bayan jihar Kano.
“Na ji daɗin kasacewa kana aiki tare da rundunar Askarawan Zamfara ta CPG. Ina so ka sani, kafin a zaɓi Askarawan Zamfara sai da Hukumar tsaro ta DSS da sauran hukumomin tsaro suka tantance su.
“Muna bayar da cikakken goyon bayan mu ga sojoji a ƙoƙarin su na yaƙi da ‘yan bindiga. An tura waɗannan jami’ai zuwa yankunan su. Muna da yaƙinin cewa sojoji a jajirce suke wajen magance matsalar tsaro.
“Zan yi amfani da wannan dama wajen miƙa ta’aziyyata bisa jajirtattun jami’an da suka rasu a hanyar Gusau zuwa Funtuwa. Allah gafarta masu. Ina tabbatar maka da cewa gwamnatina na tare da kai, kuma za mu ci gaba da aiki tare da jami’an soji da sauran hukumomin tsaro don kawo ƙarshen ‘yan bindiga.”
Tun farko a jawabinsa, Babban Hafsan Tsaron Ƙasa, Janar Christopher Gwabin Musa, ya nuna matuƙar godiyar sa ga Gwamna Dauda Lawal bisa goyon bayan da ya ke bai wa sojoji da sauran jami’an tsaro a jihar. “Mun zo nan ne don muna godiyar mu bisa irin goyon bayan da ka ke bai wa sojoji da sauran jami’an tsaro, tare da irin gagarumar ci gaban da kake samarwa a jihar Zamfara.
“Na kasance ina alfahari da Gusau da na sani, amma gaskiya, yanzu abin da na gani, sai na rasa me zan ce. Yabon gwani ya zama dole bisa irin ci gaban da ka samar wa Zamfara a shekara ɗaya kacal, a ƙarƙashin jagorancinka. Ina gode maka bisa inganta rayuwar al’umma. Wannan romon Dimokraɗiyya ne. Muna ganin ci gaba da dama, tare da wasu ayyukan da ake gudanarwa a jihar, tun bayan hawan ka mulki.”