A cewar wani binciken da BBC ta gudanar kan shaidun da suka hada da rahotannin sojojin Birtaniya, da sakonnin imel, da hotunan ramukan harsashi a wurin, mambobin tsohon runkunin soja na musamman na Birtaniya dake Afghanistan, sun sha kashe fursunoni da fararen hula da ba sa dauke da makamai, har ma su kan yi gasar kisan mutane, daga cikinsu, akwai yiwuwar wata runduna ta kashe mutane har 54 ba bisa ka’ida ba, a wa’adinsu na watanni 6 a wurin.
Bayan fallasa wadannan laifuffuka, ma’aikatar tsaron Birtaniya, ba ta nemi afuwa ba, kuma ba ta dauki alhakinta ba, amma ta yi kokarin yin rufa-rufa, tana mai zargin rahoton BBC da “labaran da ba su dace ba kuma wai ba daidai ba ne”.
Hasalima, ba sojojin Birtaniya ne kawai suka kashe fararen hula ba gaira ba dalili ba. A watan Disamba na shekarar 2020, ma’aikatar tsaron kasar Austriliya, ta fitar da rahoton binciken game da kyamar bil-Adama da sojojinta suka yiwa fararen hula a kasar Afghanistan.
Game da Amurka kuwa, mamayar da aka yi a kasar Afghanistan na tsawon shekaru 20, ta yi sanadiyar rayukan ‘yan kasar dubu 174, ciki har da fararen hula dubu 30.
Wadannan kasashe suna ikirari kare hakkin Bil Adama a ko da yaushe, to yaya za su bayyana kisan gillar da suke yiwa mutanen da ba su san hawa ba balle sauka a kasashen waje?
Yarjejeniyar Geneva ta bayyana a fili cewa, ba daidai ba ne kisa, tilastawa, muzgunawa da ma korar mazauna zaman lafiya haramun a lokacin yakin, kuma wadanda ba su taka rawa a yakin ba, za a mutunta su a kowane hali.
Amurka da Birtaniya da Austriliya, dukkansu sun sa hannu kan wannan yarjejeniya, amma sun sha keta dokokin kasa da kasa. Sun zama masu kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.
Laifukan da suke aikatawa, laifi ne ga daukacin bil-Adam, don haka a cancanci a yi musu adalci. Dole ne kasashen duniya su yi adalci ga wadanda ba su ji ba ba su gani ba. (Amina Xu)