Shugaban kwamitin Rundunar Soji a Majalisar Dattawa, Sanata Muhammad Ndume ya bayyana cewa akwai bukatar a binciki Bankin Ci Gaban Nijeriya watau Development Bank of Nigeria (DBN) da Gwamnatin Tarayya ta kafa domin taimakawa kananan masana’antu da `yan Kasuwa sakamakon zargin gudanar da al’amura ta hanyar da bata dace ba.
Ndume wanda ya kasance mamba a cikin wani kwamitin na wucin gadi na mutane bakwai da Sanata Muhammad Sani Musa 313 ke jagoranta a Majalisar Dattawan Tarayyar, ya yi nuni da cewa a wani binciken da suka yi alamu na nuni da cewa kwalliya ba ta biya kuɗin sabulu ba.
Ya kara da cewa an kawo Kudirin Dokar ne domin a binciki Bankin ta DBN wanda Gwamnatin Tarayya ta kafa saboda tabbatar da an taimaka wa kananan `yan Kasuwa da masana’antu domin su samu tallafi mai sauki ta yadda za su farfado ko su kafa kananan masana’antu wanda yake da mahimmaci ga masu kananan karfi domin idan aka farfado da wannan `yan Kasuwa da masana’antu shi ne za a iya farfado da tattalin Arzikin Kasar.
Ya ce “amma abun takaici shi ne mun lura a cikin wani bincike cewa Bankin DBN a cikin shekarar 2021, ta rabar da kudi kusan kimanin rabin Tiriliyan, amma abun takaici shi ne inda talauci ya fi katutu kuma inda ake bukatar a farfado da kananan masana’antu ba su samu ko rabin abin da suka rabar ba.
“Na gano cewa Jihar Legas kadai a cikin Kudi naira Biliyan 483 sun samu kashi 47% amma sauran shiyyar Kudu maso yamma sun samu kashi 10 wanda gaba daya kudin ya kama naira Tiriliyan 274 a yayin da daga cikin Jihohi shida na Kudu maso yamma, ita Jihar Legas kadai ke da Kudi kimanin naira Biliyan 227 amma sauran Jihohin biyar ke da kashi 10.
“Haka Kudu maso Kudu sun samu kashi 17 da ya kama Naira Biliyan 81, amma gaba dayan Arewa da ke da Jahohi 19 sun samu kashi 11 wanda ya kama kimanin naira Biliyan 53, domin a shiyyar Arewa maso gabas ta samu kashi 5 wato naira Biliyan 24, sai shiyyar Arewa maso yamma ta samu kashi daya wato Naira Biliyan 4,820.
“Makasudin kafa wannan Bankin shi ne don ta taimaka wa kananan `yan Kasuwa da masana’antu wanda sune ke fannin Noma, kasuwanci, sufuri amma sai muka ga sun dauki kashi 42 na kudin sun ba masu harkar mai.
“Kudin da aka bayar ga shiyyoyin 6 bashi ne ake bayarwa mai sassauci don farfado da tattalin Arzikin Kasa ta hanyar Bankin don ita Bankin da za ta bayar, ba tana bayarwa ba ne don riba sai don a taimaka.
“Misali a Jihar Kano da Sokoto an rufe masana’antu da yawa don ba Kudin da za a farfado da su, shi ne ya sa ake so a basu wannan kudin da zai zamanto ba za a kuntata musu ba, toh amma kwalliya ba ta biya kuɗin sabulu ba.
Acewarsa, akwai bukatar a yi bincike don sanin shin nawa ne Kudin, mai yasa aka rabar da kudin haka, meye za ayi don tabbatar cewa dalilin da ya sa aka kafa wannan Banki da kuma tabbatar da cewa Kudaden da ake rabar sun je ga hannun wadanda ya kamata, kuma `yan Nijeriya su gani a kasa ta hanyar tabbatar da cewa kananan masana’antu na tasowa ta hanyar taimakon wannan Banki tunda a bisa wannan dalilin ya sa aka kafa Bankin na DBN.
“Kuma akwai Bankin Kasuwanci (BOI), NIRSAL ta CBN da Gwamnatin Tarayya da suka sha fitar da wadansu hanyoyin da tsari don taimaka wa `yan Nijeriya talakawa amma har yanzu ba a gani a Kasa ba saboda matsalar wadanda aka saka su su yi aikin ya sa muke son mu yi bincike a Majalisar domin idan da akwai wadanda suka hana ruwa gudu, sai a san yadda za a yi a kawar da su domin a samu tsari mai kyau a kan abin da ake bukata.
“An hada kwamitin wucin Gadi na mutum bakwai, an saka ni member kuma Inshaa Allah za mu tabbatar da cewa an yi abun da ya dace don tabbatar da cewa `yan Nijeriya sun ga abin da aka yi tare da tabbatar cewa an yi maganin matsalar.
“A yanzu talauci ya addabi `yan Nijeriya musamman Arewa. A kiyasi, Jihar Kebbi na fama da talauci kimanin kashi 86, Jihar Gombe 77, Jihar Bauchi 87, Jihar Taraba 78, Jihar Zamfara kashi 80, sannan kusan rabin Jihar Filato na fama da talauci, haka sama da rabin `yan Jihar Ebonyi su ma suna fama da talauci, shi yasa ni a matsayin wakili na kai wannan lamarin gaban Majalisar don a yi wa tubkar hanci, a yi maganin lamarin kuma `yan uwana `yan majalisar sun karbi abun hannu biyu-biyu, don haka suka bani goyon baya.” Inji Ndume