Alhaji Abdullahi Yaluwa Ajiyan Yawuri, shi ne shugaban ‘yan Arewa masu mallakar gidajen Rediyo da Talabijin. A tattauanwar da ya yi da wakilinmu, ya bayyana matsayar kungiyarsu a kan yadda aka wulakanta yara kanana da sunan gurfanar da su a kan shiga zanga-zangar tsadar rayuwa watanni 6 da suka wuce. Ga dai bayanan da ya yi.
“Makasudin wannan labari da muka fitar shi ne bayan mun ga hotuna a Soshiyal Midiya da yara kanana, duk wanda ya dube su za ka ga tsoro da barazana a fuskokinsu, da yunwa da kuma shida ta cewa an tirsasa musu da wuya, an kuma yi amfani da tsari na yunwa, kuma babban abin tambaya ma yanzu shi ne, su wadannan da Allah ya sa aka gani kila su Allah ya yi musu gyadar dogo, to me ya samu sauran da kila Allah bai nufa su an kawo su kotun ba?
- NAHCON Za Ta Biya Alhazai Diyyar Wasu Kuɗaɗe Kan Ƙarancin Kula Da Su Lokacin Hajji
- EFCC Ta Gurfanar Da Tsofaffin Gwamnoni Da Tsofaffin Ministoci, Bayan Kwato Kadarorin Biliyoyin Naira A Kasashen Waje
“To babu shakka wannan tsari na shugabancin rashin gaskiya da muka gani dole ya tayar wa kowa hankali ba a Arewa kawai ba a duk duniya, kuma ya nuna cewa a karkashin wannan shugabanci na Bola Ahmed Tinibu Nijeriya fa ta kama hanyar lalacewa, kuma babu yadda za a yi mu kira kanmu da kasa mai aiki da Dimukradiyya.
“To wadannan yara an zarge su ne wasu daga cikinsu dai yan shekaru 12 wasu 13 wasu 14, an zarge su wai da yi wa Nijeriya zagon kasa, to ka dubi wadannan yaran ka ce wai su ne su kai barazanar tunbuke gwamnatin Tinubu, to ka san babau shakka akwai rashin hankali a wannan zaton.
‘’Kuma abin da yake bani mamaki shi ne, gwanati da ta ce tana da masaniya akan mutanen da suka assasa wannan zanga-zangar ta #EndBadGobernace# har yanzu ba a kawo su kotu ba sai wadannan yara wanda yawancin su ma idan a wajen zanga-zangar aka kama su, to sun tafi tafi ne kawai a matsayin yaro ya ji abin hanyaniya ya ruga ya gani kuma wannan a gidan kowa akwai irin su.
Mun yi kira ga gwamnati da ta saki wadannan yaran kuma ta tabbatar da an kiyaye lafiyarsu, kuma wadanda ba su da kafiya muna kira ga gwamnati ta fita da su kasar waje kamar yadda shugaban kasa ke fita a kai su Faransa a kai su Ingila domin a duba lafiyarsu, kuma a biya su diyya, sannan duk wani wanda ke da hannu a cikin wannan ta’asar daga Babban Sufeto Janar na ‘Yansanda zuwa mai shari’a, lauyoyin gwamnati ma, to duk wanda ke hannu a wannan Fir’aunancin, muna kira ga gwamnati ta kama su a yi wani kwamiti da za ta bicike su kuma wanda aka kama da laifi a horar da shi. mun jaddada wa gwamnati cewa, matsaloli da Nijeriya ke ciki ba ‘yan Nijeriya suka jawo shi ba, tsarin shugabancin wannan gwamnatin ne ya kawo wadannan matsaloli, kuma ‘yan Nijerita ba za su daina fitowa zanga-zanga ba domin wadanda ke shugabancin mu yanzu ba su fi mu zama ‘yan Nijeriya ba.
“Bayan haka, muna neman cewa tsare-tsare na gwamnati dake kawo mana bala’i, da jawo mana fakirci, dake sa mutane suna mutuwa a gidansu da yunwa, to muna kira ga gwamnati ta janye wadannan.
“Maganar tallafi akan fetur, maganar tallafi akan biyan biyan kudin wuta, maganar tallafi akan sauran abubuwa na gwamnati da wasu kasashe ke yi, ko kasashen da ke amfani da jari hujja ba su daina ba da irin wannnan tallafin ba, muna kira ga gwamnati ta janye wadannan tsare-tsare kuma a dawo mana da tsarin da muka amince domin su ne shugabannin, amma mu ake shigabanta, kuma yadda za a ce ra’ayinmu bai da wani muhimmanci akan yadda gwamnati za ta gudanar da shugabancinta, mun gaji da ba mu hakuri, “Mun gaji da gafara sa muna so mu gani a kasa, ita ce babbar magana kuma shi ne babban kiran da muka yi ga gwamnati”.