Kocin Real Madrid Carlo Ancelotti ya ce kamata ya yi a dakatar da dukkan wasannin kwallon kafa a Sifaniya bayan ambaliyar ruwa da ta afku a Balencia wanda ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 217, wasan LaLiga na Madrid da Balencia wanda za a buga ranar Asabar an dage shi, tare da wasan Billarreal da Rayo Ballecano, amma an buga sauran wasanni takwas na La liga.
La liga na hada kai da kungiyar agaji ta Red Cross don tara kudade ga wadanda ambaliyar ta shafa, bayan da dubban gidaje da wuraren kasuwanci suka lalace, da kuma katse hanyoyin sufuri, a daya daga cikin bala’o’i mafi muni a tarihin Sifaniya na baya bayan nan.
- Shugabannin Sin Da Italiya Sun Kalli Kayayyakin Tarihi Da Aka Dawo Da Su Kasar Sin
- Yadda Donal Trump Ya Lashe Zaben Shugabancin Amurka
Muna cikin bakin ciki, in ji Ancelotti a wani taron manema labarai muna tare da Balencia da duk garuruwan da abin ya shafa, da fatan za a iya magance wannan matsala nan ba da jimawa ba, domin hakan ya shafe mu sosai in ji shi.
‘Yan wasa da masu horar da ‘yan wasa da dama sun ba da shawarar cewa ba wasan kwallon kafa da ya kamata ya gudana a Sifaniya a karshen mako, inda kocin Atlético Madrid Diego Simeone suka ce shawarar ci gaba da buga kwallo a cikin wannan yanayi da ake ciki ba ta da wata ma’ana.