• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ya Kamata A Kirkiro Da Ma’aikatar Kula Da Harkokin Fulani – Bello Badejo

byIdris Aliyu Daudawa
3 years ago
Fulani

Shugaban Kungiyar Miyetti Allah Kyautal Hore na Kasa, Abdullahi Bello Badejo ya bayyana cewa ya kamata gwamnatin tarayya ta samar da ma’aikatar kula da harkokin Fulani.

Shugban ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kamma wani da taro da ya shafi Fulani mai taken ‘Fulani ina mafita.’
Ya ce taron yana da matukar muhimmanci a al’amuran da suka shafi Fulani, kuma taron ya gudana ne har kashi biyu.

  • NNPP Ta Yi Sabbin Kamu A Jihar Kaduna

A cewarsa, Fulanin Nijeriya suna fuskanta matsaloli daban-daban, shi ya sa suka ga ya fi dacewa su nemi Fulani su nuna masu cewa suna tare da su dari bisa dari tare da nuna musu cewa lalle suna da shugabanci da kuma wakilci, domin kar su dauka ba su da shugabanci ko kuma wakilci.

Ya kara da cewa sun nemi masu ruwa da tsaki wanda suke da ilimin zamani daga cikin Fulani da masana kan kiwon dabbobi a Nijeriya wadanda aka yi su shekaru da suka gabata, domin su bayar da shawarwari kan matsalolin da suka shafi Fulani a Nijeriya.

Ya nuna farin cikinsa bisa amsar goron gayyata na masu ruwa da tsaki kuma har sun tofa albarkacin bakinsu a wurin wannan taro.

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Dauda Lawal A Shekara 60: Inda Akwai Fata, Akwai Mafita

GORON JUMA’A

Shugaban kungiyar ya ce babu wani da zai kasance shugaba ko sarki ya ji dadi ana rikici a jiharsa ko yankinsa.
Ya ce, “Wannan shi ya sa muke ganin wasu gwamnoni ba laifinsu ba ne kuma shi ma shugaban kasa ba laifinsa ba ne ake ta rigima, musamman ta Fulani da wasu kabilu, domin gwamnati tana da fadi.

“Mu a kungiyan Miyetti Allah Kautal Hore ya za mu yi mu shigo domin taimaka wa gwamnati da kuma hukumomin tsaro wajen dakile rikici a tsakanin Fulani da sauran kabilu.

“Mun tara Fulani fiye da 14,000 wadanda suka hada da matasa maza da mata, muna tare da su domin yi musu gargadi da nuna masu muhimmancin zaman lafiya. Kuma cikin ikon Allah ina tsammanin za a samu nasara cikin abin da muke niyyar aiwatarwa,” in ji shi.
Ya ce wannan shi ne taro na farko wanda aka tara Fulanin Nijeriya da na kasashen Afirka saboda ana kan hanya kuma kwalliya za ta biya kudin sabulu.

Ya ce sun mika bukatar a kafa ma’aikata ta kulawa da harkokin da suka shafi Fulani kamar irin wadda take kulawa da harkokin da suka shafi Neja Delta.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwamna Dauda Lawal A Shekara 60: Inda Akwai Fata, Akwai Mafita
Al'adu

Gwamna Dauda Lawal A Shekara 60: Inda Akwai Fata, Akwai Mafita

September 2, 2025
GORON JUMA’A
Goron Juma'a

GORON JUMA’A

August 15, 2025
GORON JUMA’A 8-8-2025
Goron Juma'a

GORON JUMA’A 8-8-2025

August 8, 2025
Next Post
Wuraren Shakatawa 10 Da Suka Fi Tasiri A Duniya (zamantakewa)

Wuraren Shakatawa 10 Da Suka Fi Tasiri A Duniya (zamantakewa)

LABARAI MASU NASABA

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version