“In ba mu san tarihi ba, ba za mu koyi darasi ba”. Wani ma’aikacin sa kai ne ya bayyana haka a bikin nune-nunen ayyukan da sojojin Japan suka yi a lokacin da suka kai hari kan kasar Sin cikin yakin duniya na biyu. Wata kungiyar al’umma ta kasar Japan ta shafe shekaru 10 a jere tana gudanar da wannan biki, kuma wannan maganar da ma’aikacin sa kai ya yi, ya bayyana ainihin dalilin gudanar da bikin. Yau 15 ga watan Agusta, ita ce ranar cika shekaru 80 da kasar Japan ta sanar da ba da kai ba tare da wani sharadi ba, iri wannan magana, gargadi ne a gare mu.
Manufar tunawa da wannan tarihi, ita ce koyon darasi, tare da girmama yanayin zaman lafiya da muka samu. Amma bayan shekaru 80, ra’ayoyin da kasar Japan ta nuna, sun sa ana ganin ta kamu da cutar “mantuwar tarihi”. Wasu ’yan siyasar kasar suna neman sauke nauyin dake wuyansu, har suna bayyana yakin kin jinin harin sojojin Japan da kasar Sin ta yi a matsayin “tayar da hankali”.
Cikin ’yan shekarun nan, ’yan siyasa masu tsattsauran ra’ayi na kasar Japan sun gyara tsarin zaman lafiya, yayin da suka fadada aikin soja, domin farfado da harkokin sojan kasar. Wadannan matakan da kasar Japan ta dauka sun bata tsarin kasa da kasa bayan yakin duniya, tare da kalubalantar yanayin zaman lafiya a yankin Asiya da tekun Pasifik, lamarin da ya sa, kasashe makwabta a nahiyar Asiya da gamayyar kasa da kasa damuwa sosai.
Ban da rashin fahimtar tarihi, aniyar kasar Amurka ta inganta manufar siyasarta a yanukan dake tekun Indiya da na Pasifik, ya kuma kasance muhimmin dalilin da ya sa kasar Japan ta keta tsarin zaman lafiya.
Kasar Japan ba za ta samu kwanciyar hankali ta hanyar gyara tarihi da fadada harkokin soja a kasar ba, sai ta mutunta abubuwan da suka faru cikin tarihi tare da rokon gafara, ta yadda za ta shimfida zaman lafiya a cikin kasa. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp