Bayan girgizar kasa mai karfin gaske da ta abku a kasashen Turkiyya da Syria, kungiyar yaki da wariyar launin fata ta Amurka da Larabawa ta yi kira ga Amurka da ta dage takunkumin da ta kakaba wa Syria nan take, ta yadda za a samu saukin kai kayan agaji zuwa Syriar. Sai dai, Amurka ta ce, ba za ta yi mu’amala kai tsaye da gwamnatin Syria ba.
Game da wannan batun, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a yayin taron manema labaru na yau Laraba 8 ga wata cewa, Amurka dai ta dade tana shiga cikin rikicin kasar Syria kuma ta sha daukar matakan soji, da saka takunkumi mai tsanani kan tattalin arziki, wadanda suka haddasa rasuwar fararen hula masu yawa a kasar, baya ga haka, da kyar jama’ar kasar su iya samun tabbacin zaman rayuwarsu na yau da kullum. Haka zalika ana fuskantar matsaloli masu yawa ta fuskokin ci gaban tattalin arziki da sake raya kasar.
Mao Ning ta kuma kara yin kira ga Amurka da ta yi watsi da ra’ayin siyasar duniya, kuma nan take ta dage takunkumin da ta kakaba wa Syria, tare da bude kofa ga bayar da agajin jin kai. (Mai fassara: Bilkisu Xin)