• English
  • Business News
Tuesday, November 4, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ya Kamata Birtaniya Ta Girmama Alkawarin Da Ta Dauka Game Da Batun Tsibiran Malvinas

by CMG Hausa
3 years ago
Birtaniya

Kwanan baya, ofishin jakadancin Birtaniya dake Argentina, ya gabatar da wata gasar bidiyo a kan yanar gizo, ga daliban jami’o’in dake kasar, inda ofishin ya yi ikirarin cewa, wanda ya lashe gasar zai samu damar yin ziyarar mako guda kyauta a tsibiran Malvinas.

Game da hakan, ma’aikatar harkokin wajen kasar Argentina, ta fitar da sanarwar nuna rashin jin dadin ta, inda ta ce, matakin da Birtaniya ta dauka na nufin cewa tana mallakar tsibiran, don haka ta bukaci Birtaniya da ta cika alkawarin da ta dauka karkashin kudurin MDD, kana ta yi shawarwari da Argentina game da ikon mulkin tsibiran.

  • Kasar Sin Ta Lashi Takwabin Kare Ikonta Bayan Ziyarar Da ‘Yan Majalisar Amurka Suka Kai Yankin Taiwan

A shekarar 1816, Argentina ta samu ‘yanci daga mulkin mallakar kasar Spaniya, tare da samun ikon mulkin tsibiran Malvinas, amma lokacin da Birtaniya ta habaka mulkin mallakarta a kudancin nahiyar Amurka, ta mamaye tsibiran na Malvinas a shekarar 1833.

A shekarar 1982, yakin da aka gwabza na tsawon kwanaki 74 tsakanin kasashen biyu, domin karbe ikon mulkin tsibiran, ya kai ga Birtaniya ta samun nasara. Amma duk da haka, Argentina ba ta taba yi watsi da ikon mulkin tsibiran ba.

Kwamitin hana mulkin mallaka na MDD, ya fitar da kuduri har fiye da sau 30, don kalubalantar gwamnatin Birtaniya, da Argentina, da su yi shawarwari kan batun, kuma sau da dama Argentina ta gaggayci Birtaniya da ta shiga shawarwari, amma Birtaniya ta ki karbar gayyatar.

LABARAI MASU NASABA

Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce

Birtaniya ba za ta canja ikon mulkin tsibiran ba, saboda shaiddu da ake da su game da batun, duk da atisayen soja, ko na makamai da take girkewa, ko gasar da za ta gudanar da sauransu ba.

A watan Maris na shekarar 2016, kwamitin tabbatar da iyakokin bangarorin duniya na MDD, ya ba da tabbacin cewa, Argentina na da ikon mulkin tsibiran Malvinas.

Ban da wannan kuma, kimanin dukkan kasashe dake nahiyar Latin Amurka, da yankin Caribbean, suna goyon bayan Argentina game da batun. Kaza lika ita ma kasar Sin tana marawa Argentina baya, kan ikon mulkin tsibiran. (Amina Xu)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

November 3, 2025
Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce

November 3, 2025
An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau
Daga Birnin Sin

An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau

November 3, 2025
Next Post
A Karon Farko Gwamnatin Kano Za Ta Nada Matashi Mai Karancin Shekaru Mukamin Kwamishina

“Ƴan Adawa Sun Wuce Gona da Iri — Wike Ya Soki Masu Goyon Bayan  Trump

“Ƴan Adawa Sun Wuce Gona da Iri — Wike Ya Soki Masu Goyon Bayan  Trump

November 3, 2025
Shugabannin Wasu Kasashe Za Su Halarci Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas A Birnin Shanghai

Shugabannin Wasu Kasashe Za Su Halarci Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas A Birnin Shanghai

November 3, 2025
Li Qiang Zai Halarci Bikin Bude Taron CIIE Na 8 Da Sauran Ayyuka

Li Qiang Zai Halarci Bikin Bude Taron CIIE Na 8 Da Sauran Ayyuka

November 3, 2025
Likitocin Gwamnati Sun Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yaɗa Bayanai Na Karya

Likitocin Gwamnati Sun Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yaɗa Bayanai Na Karya

November 3, 2025
Bikin Baje Kolin CIIE Zai Samarwa Najeriya Karin Damammaki

Bikin Baje Kolin CIIE Zai Samarwa Najeriya Karin Damammaki

November 3, 2025
Chadi Ta Rufe Iyakarta Da Nijeriya Bisa Dalilan Tsaro

Chadi Ta Rufe Iyakarta Da Nijeriya Bisa Dalilan Tsaro

November 3, 2025
Sin Ta Yi Allah Wadai Da Illata Fararen Hula Tare Da Fatan Gaggauta Kawo Karshen Yaki A Sudan

Sin Ta Yi Allah Wadai Da Illata Fararen Hula Tare Da Fatan Gaggauta Kawo Karshen Yaki A Sudan

November 3, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.