Kwanakin baya, gwamnatin soja ta jamhuriyar Nijar ta sanar da janye kasar daga kungiyar kasashe masu renon Faransa ko OIF. Hakan ya kasance wani sabon mataki da Nijar din ta dauka, da nufin yanke huldarta da kasar Faransa, wadda ta taba yin mulkin mallaka a kasar, bayan da aka janye jakadan Faransa, da sojojin kasar daga sassan kasar Nijar.
Hakika cikin shekaru 2 da suka gabata, an tilastawa kasar Faransa janye sojojinta daga kasashen Mali, da Afirka ta Tsakiya, da Burkina Faso, gami da Nijar, kana ra’ayin “kawar da abubuwa masu alaka da kasar Faransa”, na kara yaduwa cikin sauri a tsakanin kasashen yammacin Afirka da kasar Faransa ta taba musu mulki mallaka. Duk wadannan abubuwa sun nuna wani sabon yanayin da muke ciki ta fuskar siyasar kasa da kasa.
- Jawabin Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar Sin Game Da Cika Shekaru 45 Da Kulla Huldar Diflomasiyya Tsakanin Sin Da Amurka
- ‘Yan Sa-kai Za Su Taka Rawa Wajen Kawar Da Matsalar Tsaro A Arewacin Nijeriya – Yusha’u Kebbe
Dalilin da ya sa karin kasashen Afirka ke neman katse hulda da kasar Faransa shi ne kasar ta dade tana musu shisshigi, da ci da guminsu, amma ba tare da kawo tsaro da ci gaba ba.
A fannin tattalin arziki, kamfanonin kasar Faransa sun mallaki dimbin albarkatu masu muhimmanci a kasashen yammancin Afirka, kana kasar ta shawo kan tsare-tsaren hada-hadar kudi na kasashe 14 dake nahiyar Afirka, ta hanyar kafa yankin kudin Franc a Afirka. A fannin siyasa, kasar Faransa ta dade tana nuna goyon baya ga ’yan siyasar kasashen Afirka da suka taba karatu a kasar da kuma kishinta, da neman karkata manufofin kasashen Afirka zuwa ga alkiblar da take so, ta hanyar wasu matakan siyasa da na tattalin arziki. Kana ta fuskar aikin soja, kasar Faransa ta dade tana girke sojoji fiye da 5400 a yammacin Afirka. Tun daga shekarar 1962 har zuwa yanzu, ta yi shisshigi na soja a kalla karo 25 a nahiyar Afirka.
Sai dai duk wadannan matakai na shisshigi ba su haifar da ci gaban tattalin arizki a yammacin Afirka ba. A wannan yanki, har zuwa yanzu, akwai kasashe 10 da kasar Faransa ta taba musu mulkin mallaka, wadanda ke cikin jerin sunayen kasashe mafi raunin tattalin arziki a duniya. Ban da haka, ayyukan ta’addanci na ta karuwa a yankin Sahel dake yammacin Afirka. An ce, a shekarar 2022, yawan mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren ta’addanci a yankin ya kai kashi 43% na jimillar mutanen da suka mutu sakamakon wannan dalili a duniya.
A nasu bangare, mutanen kasar Faransa sun fara tunani kan laifin kansu, ganin yadda ake kin jininsu a nahiyar Afirka. A karshen shekarar bara, majalisun dokokin kasar Faransa sun gabatar da wani rahoto, wanda ya bukaci gwamnatin kasar da ta samar da karin tallafi ga kasashen Afirka, da daukar nagartattun matakai masu amfani, da nuna dukkan bayanai a fili a nahiyar Afirka.
Wasu kafofin watsa labaru na kasar sun ma ce, “Ya kamata a canza salon huldar dake tsakanin kasar Faransa da kasashen Afirka, wadda ta yi kama da ta baba da yara.”
Ban da haka, kasar Birtaniya ma ta fara tunanin laifinta. A shafin yanar gizo ko Internet, kamfanin BBC ya nuna wani bayani mai taken “Me ya sa kasashen yamma ba su ji dadi a shekarar 2023 ba?”, inda aka ce, cikin shekara daya da ta gabata, Amurka, da kasashen Turai, da sauran manyan kasashe masu bin tsarin “Dimokuradiya”, sun gamu da rashin nasara a dandamalin siyasar kasa da kasa. Marubucin wannan bayani ya ambaci yakin da ake yi tsakanin kasashen Rasha da Ukraine. Ya ce kasar Ukraine ba ta samu biyan bukata sosai ba a yakin da take yi da kasar Rasha, wanda ya nuna mawuyacin halin da kasar Amurka da kasashen Turai suke ciki, wadanda suka riga suka samar da kudin tallafi da ya kai dalar Amurka fiye da biliyan gomai ga Ukraine din.
Ban da haka, an ce, ko da yake kasashen yamma na Allah wadai da hare-haren da kasar Rasha take kaddamarwa, a hannu guda, sauran kasashen na da ra’ayi na daban. A ganin dimbin kasashen, habakar kungiyar tsaro ta NATO zuwa yankin gabas ya tsokani kasar Rasha, abin da ya ta da yaki daga bisani.
Har ila yau, cikin bayanin da kamfanin BBC ya gabatar, an tabo maganar yakin da ya barke tsakanin Falasdinu da Isra’ila, wanda shi ma ya karya kwarjinin kasashen yamma. An ce wannan yaki ya karkata hankalin mutanen duniya daga kan abokiyar kungiyar NATO, wato Ukraine. Kana wanda ya fi muhimmanci shi ne, a ganin dimibin Musulmai da sauran gungun mutane na kasashe daban daban, yadda kasashen Amurka da Birtaniya ke neman kare kasar Isra’ila a MDD, ya nuna cewa su ma suna da jini a hannunsu, a kisan kiyashi da aka yi wa dubun-dubatar jama’ar yankin Gaza, wadanda ba su san hawa ba, balle ma sauka.
Kamar dai yadda Hausawa su kan ce, jiki magayi ne. Mutanen kasashen yamma ba za su fadi gaskiya ba, har sai sun gamu da matsala. Sai dai yadda kasashen yamma ke fama da mawuyacin hali a wurare daban daban, ya nuna bambancin da aka samu, tsakanin yadda kasashen yamma suke kallon kansu da ainihin abubuwan da suke iya yi, gami da tsakanin ra’ayin su kan abubuwa, da kuma tunani mafi samun farin jini a duniya.
Saboda haka, kamata ya yi, kasashen yamma su kara tunani kan laifukansu, don magance aikata karin laifuka, da baiwa kasashen duniya karin damammaki na samun ci gaba, ta hanyar tabbatar da zaman lafiya, da gudanar da hadin kai mai amfani ga kowa. (Bello Wang)