Mai magana da yawun kungiyar Dattawan Arewa (NEF) Dakta Hakeem Baba Ahmed ya yi nuni da cewa, ya kamata makusantan Shugaba Muhammadu Buhari su gaya masa ya yi Murabus daga mulki ganin yadda lamarin kasar nan ke ciki yanzun.
Ya sanar da hakan ne a shafinsa na Kafar sada zumunta ta Twitter, inda ya bayyana cewa, mai Yuwa a 2023 lamarin na rashin tsaro ya fi muni, ya kuma Koka kan irin karfin ikon da Buhari ya ke da shi.
Baba-Ahmed ya ci gaba da cewa, a ra’ayi na, na damu kan yadda lamarin kasar nan ya ke yanzun amma na fi jin tsoron yadda Nijeriya za ta kasance a watan Mayun 2023.
A cewarsa, idan har akwai mutanen da Buhari ya ke jin maganar su, su gaya masa ya yi murabus.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp