Kamar yadda shafin RUMBUN NISHADI ya saba zakulo muku fitattun jaruman finafinan hausa har ma da masu tasowa, kana da labaru na musamman wadanda suka shafin cikin masana’ar kannywood, a yau ma shafin na tafe da wata jarumar da ake damawa da ita a yanzu wato AISHA TAFIDA EL-NAFATY wacce aka fi sani da AISHA TAFIDA GOMBE. Inda ta bayyanawa masu karatu takaitaccen tarihinta har ma da wasu batutuwan da suka shafi sana’arta ta fim.
Ga dai tattaunawar tare da wakiliyar mu RABI’AT SIDI BALA Kamar haka: Da farko masu karatu za su so su ji cikakken sunanki.
Sunana Aisha Tafida El-Nafaty wacce aka fi kira da Aisha Tafida Gombe.
Ko za ki fadawa masu karatu dan takaitaccen tarihinki?
Ni dai haifaffiyar garin Gombe ce, nayi makarantar firamare da sakandre a “Gobernment Girls Secondary School” dake cikin garin Gombe, daga nan kuma sai na dawo Kano da zama na fara sana’ar fim.
Ya batun ci gaba da karatu akwai ra’ayin hakan a nan gaba ko babu?
Ina da burin hakan in sha Allah idan Allah ya amince.
Ya batun aure shin kin taba yi ko kuwa tukunna dai?
Na taba yin Aure inada yara 3.
Me ya ja hankalin ki har ki ka tsunduma harkar fim?
Kawai ra’ayi ne, saboda tun ina karama fim yana burge ni sai nake ji a raina kamar idan na girma ni ma zan iya yi, sai kuma Allah ya amince.
Ya gwagwarmayar shiga cikin masana’antar ta kasance?
To ni dai gaskiya ban sha wata wahala sosai ba wajen shiga fim, sai dai kalubale kawai dana samu da iyaye da ‘yan’uwa su ma daga baya sun amince kuma sun bani goyon baya sosai.
Za ki yi kamar shekara nawa da fara fim?
Shekata biyu kawai nayi ina fim dana samu miji sai nayi aure, da auren ya kare ne sai kuma na sake dawo wa fim din saboda ita ce sana’ar dana iya nake yi.
Idan na fahimce ki kina so ki ce a can baya kin taba yin fim, yanzu dawowa ki ka yi kenan, to a wacce shekara ki ka fara a wancen lokacin, kuma a wacce shekara ki ka dawo yanzu din?
Eh! haka ne, na gama sakandare dina a ‘G.G.C Doma’ dake garin Gombe a shekarar 2011, sai na shiga harkar fim 2013 kuma nayi aure, 2023 Kuma da auren ya kare sai na dawo sana’ata.
Da wane fim ki ka fara a wancen lokacin da kuma wannan lokacin da ki ka dawo?
A wancan lokacin na fara fim din ‘Wa Zai Auri Jahila’ da kuma ‘Kallo Ya Koma Sama’ na ‘Alkausar Mobies’, fim din Darakto Ibrahim Bala. Bayan na dawo kuma fim din dana fara shiga na Abubakar Bashir Meshadda ‘Ana Dara Ga Dare’ da ‘Halimatussdiyya’ da kuma ‘Hauwa kulu’.
Wane rawa ki ka taka cikin wadannan finafinan, shin ke ki ka ja ragamar shirin matsayin jaruma/tauraruwa cikin shirin ko ya abun ya kasance?
‘Wazai Auri Jahila’ na fito ne a matsayin jahila amma a fim din, wacce ba ta yi karatun addini ba, bata san yadda za ta bautawa Allah ba, wanda ko suratul fatiha bata iya karantawa ba, amma dai ta yi ilimin boko sosai sakamakon mahaifinta attajiri ne a kasar waje ma tayi karatun.
‘Kallo Ya Koma Sama’ na taso cikin maraici na rashin uwa, na rayu hannun kishiyar uwa, ta wahalar da ni sosai, amma ta nunawa ‘yar ta gata ta kyale yarinyar tana yin abin da take so wanda a karshe ta lalace ni kuma na zama mutumiyar kirki.
‘Halimatussadiyya’ kuma mu biyu ‘Ya’ya mata mahaifinmu ya Haifa (Yakubu Muhd) kuma yanada burin mu gaji sana’ar sa na tuki sai dai mata wanda a karshe dai ya aurar da ni ita kuma kanwata (Hassana Muh’d) burinta ta shiga fim ta zama ‘yar wasan hausa, ta cinma burinta amma babanmu yayi fushi da ita.
Eh! ni na taka rawa amma a sauran rol aka bani.
Kin yi finafinai sun kai kamar guda nawa?
A kalla dai guda 10 ko 15 haka.
Wane fim ki ka fi so cikin finafinan da ki ka fito, wanne ne kuma idan ki ka tuna shi ki ke da-kin-sanin yinsa, kuma me ya sa?
Na fi son fim din ‘Wa Zai Auri Jahila’ saboda da shi na fara, amma gaskiya duk fim din dana yi babu wanda nake da-na-sanin fitowa a cikinsa, saboda tun kafin nayi sai an bani labarin na karanta na ga rol din da zan yi tukuna.
Ko akwai wani kalubale da ki ka taba fuskanta bayan shigar ki cikin masana’antar a wancen lokacin har ma da wannan lokacin?
Gaskiya Alhamdulillah! ban taba samun kowanne kalubale ba, kuma na zauna da kowa lafiya ban samu abokin fada ba.
Wane irin nasarori ki ka samu sanadiyyar harkar fim?
Gaskiya ba za su kirgu ba, na samu nasarori masu tarin yawa wanda har yanzu a cikinsa nake.
Ko akwai wani abu daya taba saka ki cikin farin ciki ko akasin haka sanadiyyar fim, wanda ba za ki taba iya mantawa da shi ba?
Farin cikina daya a rayuwata da Allah ya sa aka haife ni a cikin musulunci al’ummar Annabi Muhammad (S.A.W) Alhamdulillah. Ranar damuwata kuma shi ne ranar da mahaifiyata ta rasu amma Alhamdulillah tayi kyakyakyawar mutuwa da muke kyautata mata zaton rahamar Allah ta rasu cikin azumi a goman karshe ranar juma’a kuma ta rasu ne sakamakon haihuwa gawarta tana murmushi kamar za ka yi magana ta amsa, Allah ya ji kan dukkan magabatanmu ya sa mu cika da kyau da imani idan tamu ta zo.
Ya mu’amularki take da kawayenki wadanda ku ke tare tun kafin ki fara fim, musamman a yanzu da ki ka zama jaruma?
Mu’amalar mu bata canza ba gaskiya, muna nan kamar yadda muke da su a baya.
Mene ne burinki na gaba gake da fim?
Ba ni da wani buri a fim kuma, tunda gani a cikinta ina yi a matsayin sana’a.
Wane jarumi ko jaruma ce ke burge ki tun kafin ki fara fim?
Jarumaina kafin na shiga fim Mansura Isah, Farida Jalal da kuma Ahmad S. Nuhu Allah ya ji kansa da rahama.
Ko akwai jaruman da ki ke sha’awar yin fim tare da su?
Ai gaskiya kusan duka nayi aiki da su, kuma ni duk wanda aka hada ni aiki da shi za mu yi bana zabe.
Bayan fim kina wata sana’ar ne?
Eh, ina sana’ar sayar da kayayyakin mata haka, atamfa, lesis, abaya takalma, shadda, da dai sauransu.
A gida ki ke siyarwa ko kina da wani waje na daban da ake zuwa a siya a can kamar shago da sauransu?
A gida ne, kuma na kan saya na turawa kanne na da kawayena ma duka, su sayar su ma su samu wani abu.
Ya batun soyayya ko akwai wani cikin masana’antar daya taba nuna cewa yana sonki zai aure ki?
A’a bana soyayya da kowa a cikin masana’antar gaskiya.
Yaushe ki ke saka ran kara yin aure?
Gaskiya tukuna babu wannan zancen a raina yanzu, Alhamdulillah tunda nayi auren har inada yara, Allah ya rayasu da imani., amma ba wai na ce ba zan sake yi ba, babu dai tunanin sakewar a kusa gaskiya.
Wacce shawara za ki bawa sauran abokanan sana’arki na fim har ma da masu kokarin shiga cikin masana’antar?
Shawarar da zan basu musamman mata a rike mutuncin kai, a dinga tuna rayuwar duniyar nan kalilance, aji tsoron Allah, a dinga tuna mutuwa kowani lokaci, kuma a dauki fim a matsayin sana’a an fi ganin Albarkar ta.
Ko kinada wadanda za ki gaisar?
Gaisuwa ga dukkan masoyana da kuma ‘yan’uwa musulmi gabadaya na gode.
Muna godiya ki huta lafiya
Ni ma na gode.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp