Assalamu Alaikum Warahmatullahi Ta’ala Wa Barakatuhu.
Jama’a barkanku da sallah da fatan an yi sallah lafiya kuma an gabatar da ibadu cikin nutsuwa da yadda ubangiji ya tsara a yi.
Maganar da zan yi a yau, magana ce guda daya wadda take shawara ce gare ku ‘yan’uwa, kamar yadda muka gabatar da ibadu a cikin watan Ramadana za a ga karya ta ragu, gulma da munafunci duk an kiyaye baki, saboda a tsira kuma a samu falala mai yawa, an kyautata zumunci, kuma an nemi yafiya an gafartawa juna.
Shawarata a nan ita ce; wannan wata mai alfarma da muka yi ibadu cikinsa, ya zamanto an dore kowane wata a cikin shekara watanninmu goma sha biyu, mu yi irin wadannan ibadun mu yi koyi, ya zamanto idan wani abu a ke yi na zunubi ko na wani laifi da a ka daina a watan ramadan to, a dore da shi.
In Allah ya so ya yarda za mu ga budi, mu ga falala, kada ka ce idan watan ramadan ya riga ya wuce ya kare ai shikkenan za ka ci gaba da ayyukan da ka saba yi na laifuka tunda wata ya riga ya kare, a’a! a kiyaye domin samun tsira ranar gobe kiyama.
Ina mai kara bawa ‘yan’uwa shawara kan cewa; Dan Allah dan Annabi darussan da muka gani a watan ramadana mu dore da su, mun kyautata, mun yi sadaka, mun taimaki marayu, mun yi ibada, mun yi sallolin dare, to mu dore, mu daure, mu ci gaba da su, za mu ga canji, kuma za mu ga ci gaba.
Ina kara kira ga iyaye yadda suka rika saka ‘ya’yansu suka rika yin ibadu na dare da yin sallah a kan lokaci saboda azumi to ya kamata a dore a hakan, kada a ce sai lokacin azumi za a yi ibada, kada ka ce sai lokacin azumi kawai za ka tashi ‘ya’yanka a yi sallar asubha, a yi sallar dare, a roki Allah subhanahu wata’allah, to a dore a haka.
Haka kuma ina kara kira ga ‘yan’uwa musulmi akwai sittisshawwal falala ce mai girma a wannan azumin duk da cewa ni ba malami bane amma ina ba mu shawara da mu daure mu yi su, zai taimaka mana, kuma zai cike mana irin laifukan da muke da su na lada da muke nema.
Ubangiji Allah ya karbi ibadunmu, Amin.