Tsohon Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Nijeriya, Mohammad Babandede, ya yi kira ga Shugaba Tinubu da ya yi la’akari da kulla alaka ta kut-da-kut tsakanin Hukumar Kwastam da ta Kula da Shige da Fice.
Babandede ya yi wannan kira ne a wata hira ta musamman da ya yi da mujallar Migrationwatch.
A cikin hirar, ya ba da misali da abin da ya faru a Amurka na ranar 11 ga watan Satumba, wanda ya kara kusanta Hukumar Shige da Fice da ta Kwastam ta kasar da juna, sai dai kash! Ya yi nuni da cewa, a duk lokacin da aka yi yunkurin kusanta hukumomin biyu da juna a Nijeriya, daya sai ya rika guje wa daya.
- Ministan Yaɗa Labarai Ya Taya Janar Babangida Murnar Cika Shekaru 84
- Tinubu Ya Nada Ɗan Babangida A Matsayin Shugaban Bankin Manoma
A cewar Babandede, mutumin da ke dauke da kaya da kuma mutumin da ke balaguro ba su da bambanci iri daya ne, musamman a yankinmu. Ba za ka iya raba motsin kaya da na mutanen da ke dauke da kayan ba. Wannan ya bayyana dalilin da ya kamata Hukumar Shige da Fice da Kwastam su karfafa kawance da alakar aiki don cimma nasarar inganta tsaro da kula da kan iyakokin kasa. Ya dace manyan hukumomin gwamnatin guda biyu su kirkiri wani tsari na ayyukansu tare da hada kai don tabbatar da yaki da laifukan da ake aikatawa a kan iyakoki.
Tsohon shugaban hukumar shige da ficen ta kasa, ya kuma koka da abin da ya kira babban sakacin da ake yi da irin rawar da shige da fice ke takawa a harkokin gudanarwar Nijeriya, sannan ya bukaci gwamnatin tarayya da ta ci gaba da tallafa wa kokarin da Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya ke yi wajen inganta kula da kan iyakoki, yana mai jaddada bukatar cewa, ya kamata Nijeriya ta kafa yankunan tsaro da kuma kara hada kai da kasashe makwabta.
“Iyakar kasa ba wai kawai yanki ne na tsaro ba. Yanki ne na al’adu; yanki ne na tarihi; haka nan ma yanki ne na tattalin arziki. Kula da shige da fice na da matukar amfani ga ci gabanmu. Wajibi ne Nijeriya ta zuba jari a kan kula da nau’in mutanen da take tacewa wajen shiga kasa da kuma irin mutanen da muke tacewa wajen fita daga kasa.
“Dole ne mu yi nazarin nau’in ayyukan da bakin-haure ke yi da kuma yadda suke shafar tattalin arzikinmu. Muna bukatar tsame mutanen da ke kawo cikas ga ci gabanmu”, in ji Babandede.














