- Asarar Da Aka Tafka Sakamakon Takunkumin
- Akwai Kasashen Da Ke Neman Sharar Nijeriya Su Saya
- Tinubu Ya Dau Hanya Da Ya Yi Wa Jakadun Nijeriya Kiranye
- Mun San Wadanda Suka Saci Kudin Cibiyar Kasuwancin Nijeriya A Dubai
A makon nan, murna da farin ciki sun lullube ‘yan kasuwar da ke safara a tsakanin Nijeriya da Hadaddiyar Daular Larabawa sakamakon dage takunkumin da kasar ta kakaba wa ‘Yan Nijeriya. LEADERSHIP Hausa ta tattauna da Shugaban Cibiyar Kasuwancin Nijeriya Da Ke Dubai, ALHAJI ALIYU BAIWA, inda ya yi bayani dalla-dalla a kan yadda matsalar ta faro da kuma hanyoyin magancewa daga tushe. Har ila yau, akwai wasu boyayyun abubuwa da ya bayyana game da al’amarin tare da waiwaye a kan manufofin hulda da kasashen waje na gwamnatocin Janar Yakubu Gowon da Janar Ibrahim Babangida (masu ritaya) wanda ya ce ya kamata shugaba mai ci ya rika tuntubarsu domin shawarwari. Ga jawaban da ya yi kamar yadda RABI’U ALI INDABAWA ya rubuta mana:
Shimfida game da batun….
Assalamu alaikum Warahmatullahi Ta’alah Wabarakatuhu. Ina so na mika godiyata ga wannan jarida LEADERSHIP ta Turanci da ta Hausa, ina mai farin ciki da godiya da kuka neme ni in ba da tawa shawarar daidai gwargwadon abin da na sani da zai taimaka wa Kasar Nijeriya, bude wannan harkar kasuwanci da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi da Daular Larabawa. Ina mai matukar mika godiyata a madadina da madadin ‘Nigerian UAE Chambers of Commers’, da kuma ‘Nigerian Trade Centre, Dubai’, wanda har yanzu tana nan a matsayinta, amma akwai ‘yar tangarda tsakaninmu da mutanen ofishin jakadanci, wanda ba da jimawa in sha Allahu hukumomi da ya kamata su shigo cikin al’amarin nan za su shigo a kan wannan magana ta ‘Nigerian Trade Centre’.
Na biyu ina maia isar da ta’aziyyata ta rasuwar wanda ya kafa wannan gidan jarida mai albarka mai daraja a Arewa, ina yi masa fatan rahama ga Ubangiji. Ina kuma isar da godiyata ga babanmu Janar Yakubu Gowon, Janar Yakubu yana nan a raye. Ina isar da godiyata kuma ga Janar Ibrahim Babangida, Allah ya yi masa albarka, ina isar da godiyata ga Shugaba Jonthan Goodluck.
Wadannan mutane guda uku shugabannin ne masu adalci masu gaskiya, Allah ya sa suna raye za su ji wannan maganar tawa saboda su sun san abin da suka yi na daukaka sunan Nijeriya, to ina rokon Allah ya saka musu da alheri, ina kuma rokon shugaban kasa Ahmed Bola Tinubu ya ji shawarar mutanen nan guda uku da na lissafa, suna son Nieriya, suna da kishin Nijeriya ana daraja su a duk duniya, ina rokon sa da ya saurari mutanen nan a kan maganar da ta danganci Nijeriya da kasashen waje.
Ina isar da godiyata kuma ga Injiniya Mustapha Bello, wanda yana cikin mutanen da suka karfafa aka bude Nigerian Trade Centre a Dubai zamanin yana ministan kasuwanci, ina isar da godiyata ga mai girma Sule Lamido, lokacin yana Ministan Harkokin Waje. Wadannan mutane sun yi iya kokarinsu su ga cewa dangantar Nijeriya ta Dubai ta karfafa, Allah ya saka musu da alheri.
Maia Girma Janar Buhari, Allah ya saka masa da alheri, yana da kyakkyawan nufi, amma mutanen da suka zo suka kewaye shi su ne suka bata masa suna a kasashen waje da Kasar Nijeriya, Allah ya saka masa.
Abin da ya sa na ce a nemi shawarar su Gowon…
Lokacin mulkin Shugaba Gowon, ya taimaka wa kasashe da yawa, shi ya sa suke ganin kimar Nijeriya da shi kansa. Duk abin da zai nema za su iya yi masa alfarma a kai.
Bari in fada muku wani sirri da mutane da dama ba su sani ba, idan Janar Gowon zai tafi Amurka, akwai hanyar da shi kadai ake bari ya bi ta saboda darajarsa. Ba kuma kowane shugaban kasa ake yi wa wannan ba, shi kadai ne a cikin shugabannin da aka yi na Afirka ake bari ya shiga wannan wuri ya fita. Idan ka tafi Birtaniya har gobe ana girmama shi. Duk zargin da aka yi masa na satar kudi har yau babu wanda ya taba nuna ga inda ya saci kudin ya kai tun bayan shekaru nawa da barinsa mulki har yau.
A lokacin da na kawo wannan harka da za a kafa ofisoshi na bunkasa harkar kasuwanci a Nijeriya, da na yi masa bayani, na dauki takardun duka na ba shi, ya ce Alhaji Baiwa wannan harka ce mai kyau kuma zai taimaka wa Nijeriya, saboda haka ni zan ba da gudunmawa, duk yadda za a yi zan yi magana da Shugaban Kasa Goodluck domin a aiwatar. Wallahi kuma ya yi hakan. Da hannunsa ya rubuta takarda, ya sa hannu a kai kuma ya mika wa Shugaba Goodluck hannu da hannu a lokacin. Kuma alkawarin da na yi da Goodluck lokacin shi ne ya ce duk wani abu da zan yi na kawo ci gaba a Nijeriya in fada masa zai sa a yi kuma shi ma ya yi.
Da muka samu tangarda da mutanen Embassy (ofishin Jakadancin Nijeriya a Dubai) a kan satar kudin da suke yi, na kai kara, wadanda ya kamata su sa baki suka ki, na kai maganar ga Shugaba Babangida. Ya ce to babu damuwa, in sha Allahu wadanda suke cikin al’amarin zai kira su ya yi musu magana, kuma ya yi musu din.
Idan ka dubi Foreign Policy (manufofin hulda da kasashen waje) na Yakubu Gowon, da na Janar Babangida sun yi daidai da juna. Saboda haka idan ka duba duk wadannan abubuwan, za ka ga mutane ne da suke da kishin Nijeriya. Babu kasar da za ka tafi a duniya ka ce kai wakilin Babangida ne da ba za a karbe ka da mutunci ba.
Akwai wani sirri da zan fada muku yau, akwai ‘Yan Nijeriya da suka wulakanta a kasar Misra, Babaginda ya sayi gida ya baya rya ce ‘Yan Nijeriya su rika sauka a ciki. Babu wani shugaban kasa da ya yi wa ‘Yan Nijeriya irin wannan gatar amma mutane ba su sani ba kuma ba a fada. Akwai ‘Yan Nijeriya da ke wahala a Faransa wadanda Babangida ya saya musu gida su rika sauka.
Ire-iren wadannan shugabannin namu ya kamata a rika tuntubarsu, saboda sun san sirrin rayuwa na kasashen duniya. Sun yi mulki da tsari wadanda duk lokacin da ka je wata kasa ka ce kai Dan Nijeriya ne za a saurare ka, amma yau fa? Shi ya sa muke farin ciki da zuwan da Shugaba Tinubu Hadaddiyar Daular Larabawa domin gyara matsalar da aka samu. Kuma cikin dan kankanin lokaci ya samu gagarumar nasara, duk ma a kan hanya yake, ya ce bari ya tsaya ya dan duba wannan matsalar kafin ya dawo na musamman. Kuma muna kara ba shi shawara, tun da Allah ya sa wadannan dattawa hazikai suna raye, ya rika tuntubarsu da neman shawarwari, za a samu ci gaban kasa da ake fatan gani.
Babu kasar da Dubai ke jin dadin mu’amala da ita kamar nijeriya…
Akan maganar harkar Dubai, United Arab Emirate Dubai da Nijeriya, babu kasar da mutanen United Araba Emirate suke jin dadin mu’amala da su ta harkar kasuwanci da zamantakewa kamar mutanen Nijeriya. Mutanen United Arab Emirate, suna kaunar mutanen Nijeriya, suna daraja mutanen Nijeriya, suna daraja duk wani bakin mutum amma sun fi daraja mutanen Nijeriya.
Duk wanda yake cewa ana wulakanta shi, mutanen United rab Emirate suna wulakanta shi ni na ce karya ne, saboda zan ba da misali da kamar abu guda uku da wanda ni ko a kasata Nijeriya ban samu irinsu ba amma na samu a nan, ba ni kadai muka mutane da yawa wanda a gabana a ka yi.
Na daya dana bai da lafiya za mu tafi asuba rashin lafiya, kaninsa ya kira motar asibiti, (Ambulance) kafin minti 15 Ambulance din suna kofar gidanmu, suka dakko shi daga gidanmu suka sa shi a motar sai da suka yi wajen minti 10 suna duba shi a kofar gidanmu, sai kaninsa ya ce zai bi su tare suka ce masa babu amfanin bin mu, suka wuce da shi suka ce ga asibitin mu neme su gobe lokaci kaza a asibitin suka wuce da shi, Naira daya ba su tambaye mu ba, babu wani abu da suka tambaya, lafiyarsa kadai ita ce muhimmin abu a gare su, in ba kasar Dubai ba wace kasa ce za a yi maka haka kai da kake bako. Aka tafi da shi asibiti, ba mu tafi asibitin ba sai washe gari, muka je asibitin suka ce an shigar da aiki ba za ma mu gan shi ba sai ya farfado saboda an yi masa allura, Dirham daya ba a ce mu biya ba balle a ce ka kawo wani abu. Aka yi masa aiki kwanansa biyu a asibiti, ran na uku suka ce za a sallame shi sannan suka ce ga bill dinmu, muka ce nawa bill dinmu suka bill dinmu ya kama misalin Dala 2500, aikin da aka yi masa, suka tambaye mu yana da Inshora? Na ce ba ya da Inshora, suka ce to shike nan mu je sahen kudi, muka je, Balarabe ne Akawun a wajen, sai kaninsa ya yi masa Larabci ya ce gashi-gashi ga halin da muke ciki an bamu bil Dala 2500 muna neman a yi mana ragi, sai suka ce mu je wurin shi shugaban da ke lura da wajen, muka je wurinsa muka ce muna son a yi mana ragin bil din kudin da aka yi masa aiki, suka ce nawa za mu iya biya? Muka ce za mu biya Dala 500, ya ce Dala 500 ya yi kadan, muka ce mu abin da za mu iya biya kenan, ya ce to ku biya Dala 600, aka rage mana Dala 1900, wannan gata ni ban same shi a Nijeriya ba.
Na biyu, akwai wani dan Nijeriya da ya zo na je ziyararsa a Otel din da ya sauka, (Allah ya yi masa rasuwa Allah ya jikansa), dan Wazirin Jama’a marigayi, muna dakinsa a Otel sai ya fara aman jini, na dauki waya na kira ‘reception’ na ce ga bakonku ba shi da lafiya, suka kira Ambulance kafin minti 10 Ambulance suna karkashin Otel dinsu, aka dauke shi, Passport dinsa kawai aka ce a gani aka kai shi asibiti, in ba a kasar nan ba, ba in da za ka je a cuci kowane irin kabila kake ba a fitar maka da hakkinka ba, komai girman mutum in kana da gaskiya sai an fitar maka da hakkinka.
To saboda haka mutanen Dubai sun karbi mutanen Nijeriya fiye da yadda mu mutanen Nijeriya muke karbar ‘yan uwanmu ‘yan Nijeriya a Nijeriya. Mutanen Dubai sun yarda ‘yan Nijeriya su shiga kasarsu duk irin bata musu kasa da suke yi da cuta da zamba da rashin mutunci, duk da haka suna bukatar ‘yan Nijeriya.
Ina so in kawo wani misali kuma, a Dubai din nan, ni din nan ana ba ni kyautar kayayyaki ba ma hukuma ba kamfanoni, su kan kira ni su ce muna so mu ba da gudunmawa a kai Nijeriya.
Asarar Da Aka Tafka Sakamakon Takunkumin…
A gaskiya Nijeriya ta yi asarar a harkar cinikayya da tattalin arziki sakamakon wannan takunkumi na biza saboda duk wani bako da ya shigo Nijeriya ba ma kamfani ba, gwamnati tana karuwa da shi. Duk jirgin da ke karkashin Daular Larabawar nan alheri ne ga Nijeriya. Dalili kuwa, idan mutum yana son hulda da wani kamfani wanda ba shi a Nijeriya, to idan kuka yi mahada da shi a Dubai, in dai daga kasashen da ba su da takunkumin biza da kasar zai fito, to sai ma ya riga ka shiga Dubai. Kuma ka ga kasa ce wanda suna da tsaro, suna da harkar na’urar zamani ta sadarwa, akwai otel-otel kowane iri kake so, akwai matakai kala-kala, suna da harkokin kasuwanci da ba ma Nijeriya ba kawai da duk kasashen duniya.
Shi ya sa Nijeriya ta yi asara. Ko babu komai, jiragen da za su rika tashi daga Nijeriya musamman wannan sabon Kamfanin Jirage na Air Peace abin ya shafe su, domin da za su rika tashi zuwa Dubai daga Nijeriya. Safarar mutane za ta karu, ko ma ba don wani abu ba, sunan Nijeriya zai kara fitowa saboda za a rika cewa jirgin na Dan Nijeriya ne.
Haka nan Jiragen Emirate da ke sauka a Nijeriya, dole su sha mai a Nijeriya, akalla duk mai fita yana biyan harajin Naira 5,000, fasinja kenan, kar ka yi maganar kudin da za su biya na share musu jirgi da na otel da suke kama wa ma’aikatansu kafin lokacin tashin jirgi, kar ka yi maganar kudin harajin amfani da sararin saman Nijeriya da suke biya, haka nan kudin ajiye jirage. Akalla idan aka duba asarar za ta iya kaiwa Naira Biliyan 100.
Haka nan duk Dan Nijeriya da ya zo Dubai ya sayi kaya dole sai ya biya harajin Kwastam. Nan ma asarar da aka yi tana iya kaiwa Naira Biliyan 50, duk wannan fa asara ce da Nijeriya ta yi sakamakon takunkumin bizar da hana Emirates zuwa Nijeriya. An wayi gari Emirates na bin sama da Dala Miliyan 300 a Nijeriya.
Bugu da kari, akwai wasu yarjeniyoyi da alkawura da aka kulla lokacin da tsohon Shugaba Buhari ya zauna da ‘yan kasuwar Dubai, su ma duka abin ya shafe su ba a aiwatar ba.
Sannan akwai wani abu babban abu da mutane ba su ganewa, shi Dan Nijeriya duk inda ya fita ya samu waje, zai yi tsayin daka wajen ganin ya samu ilimi da karin fahimta na harkar kasuwanci. Wannan ma babu kamar mutanenmu na Arewa duk da ba su cika fita kasashen waje ba sosai. Kamar wadanda suke zuwa ibada a Saudiyya, a hanyarsu ta dawowa su biya ta Dubai su bude ido da kuma haduwa da sabbin mutane domin harkar kasuwanci, wannan ma an yi asararsa. Akwai yaranmu da suke yin ‘yan kananan sana’o’i a Dubai wanda yana taimaka wa mutanenmu musamman na Arewa, sukan dan samu abin da suke turawa gida, kuma wannan takunkumi ya shafe su domin ya gurgunta su.
Wannan dadewar da aka yi rashin hulda tsakanin Nijeriya da Dubai ya kawo wa Nijeriya cikas wanda har ya shafi canjin kudin nan Dala da ake samu, saboda da dan Nijeriya yana fita ya taho Dubai to zai ka wo albarka zai ka wo kaya wanda za su wadata a Nijeriya, idan kuwa kayan nan suka wadata a Nijeriya farashi zai sakko kasa, mutanen da ake hulda da su a waje za su iya kawo sassauci saboda su suna da sassauci, za ka samu kaya wanda zai rage maka wannan wahalar ta canjin kudi, wannan din kuma zai kara sa kaya su wadata a Nijeriya wanda zai iya sakko da farashin kaya a Nijeriya.
To wadannan abubuwa suna cikin abubuwan da Nijeriya ta yi asara, babu wani wanda zai zo sa jari a Nijeriya ya so ya shiga wani jirgi ba Emirate Air Line ba ko kuma ba Etihad ba, saboda mutane ne da suke so idan sun tashi daga filin jirgin samansu ba sa so su sauka sai a filin jirgin saman Nijeriya. Wannan dama da a ce tana nan, to wannan hali da aka shiga na talauci, wallahi za a samu sassauci, yau gashi wata kusan 11 an asarar biliyoyin Naira wanda Gwamnatin Nijeriya za ta karu da su.
Wannan sai ya zama mana darasi na gyara hali. Kuma ya kamata gwamnati ta zo ta yi tsari sosai na bayar da fasfo da kula da wadanda suke fita kasashen waje.
Tinubu ya dau hanya, a yi masa addu’a…
To wannan alfarma da Shugaba Tinubu ya yi mana, muna kara gode masa, kuma muna rokon mutanen Nijeriya, yaro da babba, Musulmi da Kirista a yi masa addu’a Ubangiji Allah ya bashi ikon gyara kasa. amma kasa kam lokacin Janar Buhari an kashe kasa, idan maganar gaskiya ta zo a fade ta. Ko a Addinin Musulunci akwai annabawa da sun gaya wa iyayensu gaskiya, Alkur’ani ya ce, ko da mahaifinka ne idan ya kauce ka gaya masa gaskiya, ita gaskiyar nan da za mu rike ta da ta gyara Nijeriya.
Duk wani arziki da ake da shi a duniya Allah ya ba wa Nijeriya babu kasar da take da arziki kamar Nijeriya, Allah ya bamu jama’a ya bamu kasa, ya hada mu da kasashe, ya bamu teku ya bamu jama’a ya bamu ma’adanai, ko wacce kasa a duniya tana son ta yi harka da mutane Nijeriya, duk kasar da za ka a duniya kuma a kwai dan Nijeriya a cikinta.
Saboda haka Nijeriya kasa ce wacce Allah ya yi mata komai, idan yau shugabanninmu suka daina satar kudin jama’a to za a samu kasa. Kuma muna rokon Shugaba Tinubu da ya yi wani tsari da duk wani wanda zai shigo Nijeriya ya samu biza a filin jirgin sama ya biya a filin jirgin sama, ba sai ya je yana biya a wani a wani wuri ba.
Maganar biza mu koyi abin da kasar Kenya ta yi yau, Kenya ta bude bizarta ba wani mahaluki da zai shiga Kenya kuma ya tafi wani wuri ya nemi biza, a’a yana shigowa filin jirgin sama a nan za a bashi biza, muna rokon Shugaba Tinubu ya yi wannan tsari da gaggawa, hakan ne zai kawo mutane su zo su zuba jari a Nijeriya.
Ina kalubalantar masu cewa na ci musu kudi su kawo shaidu….
Ina so in kawo hankali ‘yan Nijeriya, na daya dai babu wanda ya kawo kudi ya ce na rike masa a Dubai ko kuma na karbi kudinsa, ko mutanen da na kawo cikin kungiyar nan babu wanda zai dakko shaida yau ya ce ga shi ya dauki kudi ya bani, idan yana da ita, ni ina ba da shawara ya tafi jaridun Nijeriya ya buga cewa gashi kudi ya dauka ya bani, ya buga a jarida saoda mutanen Nijeriya su yi hukunci, akwai wadansu ina ji suna cewa ai sun bani kudinsu ko kuma na karbi kudin wani ina juyawa.
To ina rokonku mutanen LEADERSHIP ku fid da ni daga wannan zargi ku taya ni yadawa, mutanen da suka ce sun bani kudi, ni na san mutanen da suka saci kudin ofis dina, na san abin da aka dauka na kuma san abin da aka biya, don haka ina rokonsu kafin hukuma ta bi su wadannan kudi da suka kwashe na Nigerian Trade Centre to su maida wa gwamnati kudinta, saboda sun saci kudin nan ba a bani ba, ba a yi abin da aka ce a yi da su ba.
Yau na gode wa Allah Shugaba Goodluck yana nan da ransa shi ya sa hannu a takardun nan duk abin da aka yi shi ya yi su, wadanda suka saci kudin nan mun san su kuma akwai hukuma akwai kuma takardu, kuma abin da nake so na jaddada wa mutane game da Dubai din nan shi ne, yau duk abin da kai suna tarihinsa, wallahi ko da shekara 20 ne wallahi suna da shi a ma’adanar bayanansu, akwai mutanen da na taimakawa hakkina ma basu bani ba, amma yau su ne suke cewa sun bani kudi na cuce su, to sai su fito da takardunsu, in basu fito da su ba to ni zan fito da nawa na bayyana wa kowa jama’a su gani.
Ba a taba yin shugaban Nijeriya da Larabawa suka so shi kamar Buhari ba…
Ba a taba yin shugaba da kasashen Larabawan nan suka so shi ba kamar Shugaba Buhari, sannan a ce ‘yan Kasar Dubai ba sa son ‘yan Nijeriya? mu ne ya kamata mu yi tsari irin na su, yau duk wanda zai fito daga Nijeriya, to ya zamana akwai tsari ko da ya yi wata aika-aika za a iya gane ba tare da wahala ba, an san uban mutum an san uwarsa an san yayansa, an matarka an san gidanku. To mu ba mu da wannan tsarin, yau idan muka yi wannan tsarin duk wannan ba zai faru ba. harkar kasuwanci mutanen Dubai suna son Nijeriya, kuma za su iya taimaka wa Nijeriya fiye da yadda ake tsammamni. Yau idan aka kulla zumunci na gaske wallahi mutanen kasar larabawan nan ni na san za su iya daukar kudi Dala biliyan biyu su ba wa Nijeriya kyauta, saboda sun yi a wasu kasashe, sun ba wa Egypt, sun ba wa Pakistan, me ya sa ba za su ba wa Nijeriya ba, wanda sun cewa Nijeriya tana da ma’adanai da suke bukata.
Dattin Nijeriya kudi ne, mun san masu sayen dattin nan yanzu…
Na kawo shawara yadda za a bunkasa kasuwanci a kasashe 12, ni na ba da wannan shawarar, Jonathan ya amince aka bude ya ba da kudade har yau ba a bude su ba, ina kudaden suke? Saboda haka wadanda suka ci kudin nan sun sani, kuma kamar yadda Shugaba Tinubu ya fada da mu da Kasar Dubai gida daya ne dakuna ne suka raba mu, wallahi maganarsa gaskiya ce. Saboda haka mutanen Nijeriya ina rokonku, babban ci gaban Nijeriya shi ne a bude harkar jakadanci na harkar cinikayya da kasashen waje, shi ne Nijeriya za ta girma, saboda Nijeriya tana da abin da duk kasashen duniya suna bukata in ba a bude wannan hanyar ba yaya Nijeriya za ta samu arziki, Nijeriya tana da abin da yau idan ta fito da shi za ta sayar da shi biliyoyin Naira.
Bari na kara yi maka wani karamin bayani, dattin Nijeriya kudi ne, mun san masu sayen dattin nan yanzu a kwai su a kasashen duniya, kada ma ka fito da wani kayan gona dattin kawai suke so, akwai kamfanoni mun san su muna tare da su.
Allah ya yi wa Nijeriya arziki, in ka tafi Mombila Gyambu za aza kana ko kana Kanada ne lokacin kankara, in ka tafi Ogudu range, za ka aza ko kana Australia ne, in ka tafi Maiduguri za ka aza ko kana kasar Larabawa ne, idan ka tafi Sakkwato za ka aza ko kana kasar Larabawa ne.
Allah ya yi wa Nijeriya komai, mu ne ‘yan Nijeriya ya kamata mu zauna mu yi ma kammu adalci, duk wanda ya san ya saci abin da ba zai yi amfani da shi ba wanda dan ba zai yi amfani da shi ba ya mai da taskar Nijeriya saboda akwai ranar mutuwa, in yau nkai ne gobe ba kai bane.
Ya kamata shugabannin Nijeriya da suka rike mukamai su rika duba su da suka zo ya suka ga na gaba, idan suka tafi ya na baya za su zama, ya kamata shugabannin Nijeriya da ‘yan Nijeriya mu tsaya mu yi kammu hukunci. Na gode da kuka bani wannan dama Allah ya saka muku da alheri.