• English
  • Business News
Tuesday, October 14, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ya Kimar Mace Mara Sana’a Take A Wurin Mijinta?

by Amina Usman
3 years ago
Mijinta

Duk sanda akace mutum yana da dan abun juyawa duk kankantar sa tabbas ya karawa kansa kima sannan ya ragewa kansa damuwa.

Mace mau sana’a ko a wurin dangin miji kimarta daban take balle kuma akai ga shi kanshi mijin.

  • Arewa An Sha Mu Mun Warke, Bai Kamata Mu Koma Gidan Jiya Ba – Matasan Arewa A Kudu
  • Li Keqiang Ya Aike Da Sakon Taya Murna Ga Sabon Firaministan Equatorial Guinea

To idan kuma uwargida ta maida kanta sai anci an bata to fa tabbas ta hadu da aikin jira dan kuwa duk yanda kike so kiyiwa kanki abu dole ki hakura sai an dauko an baki.

Kamar yadda aka sani uwargidan da batada kwakwarar sana’a adinga inda kaganta zaka tafita daban acikin tsara,kuma rashin dan na kashewa yana janyo abubuwa da Dama musamman a zamantakewar aure.

Abu na farko mace mara sana’a zata kasance kullum cikin kunci bata san me ke mata dadi ba musamman ma idan mijin ba mai hali ba ne sosai,zata kasance ko zamantakewar ta da miji ma babu dadi kawai sai taji tana jin haushin shi batare da yayi mata wani kwakwaran laifi ba .

LABARAI MASU NASABA

Dalilin Da Ya Sa Kashi 50 Na Ƙanana Da Matsakaitan Sana’oi Ke Durƙushewa A Nijeriya– FRC

Sana’ar Hada Sabulun Aloe Vera

Rashin sana’a na sa uwar gida ko acikin danginta ta zama mujiya ta koma kamar bare,sai abinda akaci aka bata ,ko shawara za ayi sai taga ana damawa kannenta masu dan abun hannun su amma ita kuwa ta zama bare.

Hakazalika rashin abin yi na sa uwargida ta zama ‘Depressed’ wato ta kasance cikin kuci ba tada walwala. Amma yau in uwargida zata samu dan abin juyawa zata kasance batada lokaci zama tayi tunanin banza ba lokacin ta zai kasance na juya taro ya koma sisi ne.

Kamar yadda mawakiya Barmani Choge ta ke kirari a wakarta inda take cewa ‘a kama sana’a mata zaman banza ba namu ba’ to wannan magana haka take .Uwargida in kika kama sana’a ke kanki zakiji kin fi samun natsuwa yan kananan hidimar ki ba sai kin jira miji ya zo ya miki ba.

Haka yara zaki taimakawa maigida da dan kanana hidimansu wanda dai baifi karfin ki ba, kuma ko su kansu yaran sun san ana musu in suna da dan bukatun su zakiga sun nufo ki amma ba wai in sunzo sun ce a basu kusin fensir ba ki ce to ku jira Baban ku ya dawo .Wannan yana rage daraja har a idon maigida.

Uwagidan da ta rike sana’a ko shi kanshi mijin yanda zai mata magana cikin fahimta daban ne da wacce take zaune zai an daga sai an tayar. In uwargida na juya biyar ta koma goma za taga yanayin zaman lafiya a gidan ma ya karu babu yawan gaba,babu yawan jin haushin juna ko kuma hantara.

Sana’a nasa miji ya kalle mace da daraja sa kuma kima saboda yawan bani bani ko a gidan ku ne yana jawo raini amma in kika kasance kina dan daukewa maigida wasu nauyi to fa duk duniya babu kamar ki.

Koda ace uwar gida tana hidima mijin baya nuna halin ko in kula yanuna kamar bai sani ba to fa cikin ransa ba karamin farin cikin yake yi ba dan yasan dole akwai kina dauke masa wasu tallafi.

Mata a gyara a rage zaman banza, a nemi sana’a akwai sana’o’i iri daban daban kala kala sai wanda kika zaba kamar su Dinki,turaren wuta, saida itace,saka,da dai sauran su kuma duk wanda uwar gida tasa kai zata iya kuma zata samu alheri sosai dan ta tallafawa kanta har ma da ‘yan uwanta.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Dalilin Da Ya Sa Kashi 50 Na Ƙanana Da Matsakaitan Sana’oi Ke Durƙushewa A Nijeriya– FRC
Sana'a Sa'a

Dalilin Da Ya Sa Kashi 50 Na Ƙanana Da Matsakaitan Sana’oi Ke Durƙushewa A Nijeriya– FRC

August 3, 2025
Sana’ar Hada Sabulun Aloe Vera
Sana'a Sa'a

Sana’ar Hada Sabulun Aloe Vera

February 1, 2025
Masu Harkar PoS Sun Bayyana Dalilin Karin Kudin Cire Kudi
Labarai

Masu Harkar PoS Sun Bayyana Dalilin Karin Kudin Cire Kudi

November 22, 2024
Next Post
Da Dumi-Dumi: CBN Ya Musanta Bai Wa Bankuna Umarnin Karbar Tsoffin Kudi

Da Dumi-Dumi: CBN Ya Musanta Bai Wa Bankuna Umarnin Karbar Tsoffin Kudi

LABARAI MASU NASABA

Al’ummun Kasashe Daban-Daban Sun Yabawa Shawarwarin Sin Dake Taimakawa Wajen Dunkulewa Don Hanzarta Ci Gaban Mata

Al’ummun Kasashe Daban-Daban Sun Yabawa Shawarwarin Sin Dake Taimakawa Wajen Dunkulewa Don Hanzarta Ci Gaban Mata

October 14, 2025
Majalisar Wakilai Ta Buƙaci Hukumomin Tsaro Su Kai Agajin Gaggawa A Sakkwato

Majalisar Wakilai Ta Buƙaci Hukumomin Tsaro Su Kai Agajin Gaggawa A Sakkwato

October 14, 2025
Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Ghana Da Firaministar Mozambique

Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Ghana Da Firaministar Mozambique

October 14, 2025
‘Yan Majalisa 60 Sun Yi Barazanar Ficewa Daga PDP

PDP Ta Ɗage Babban Taronta Biyo Bayan Ficewar Wasu Manyan Jiga-jigai

October 14, 2025
An Kashe Mutum 3, Wasu 7 Sun Jikkata Sakamakon Ɓarkewar Rikici A Jihar Jigawa

An Kashe Mutum 3, Wasu 7 Sun Jikkata Sakamakon Ɓarkewar Rikici A Jihar Jigawa

October 14, 2025
Rashin Tsaro A Nijeriya Ba Zai Ƙare Ba Matuƙar Ba A Samar da Ayyukan Yi Da Mulki Na Adalci Ba – Amaechi

Rashin Tsaro A Nijeriya Ba Zai Ƙare Ba Matuƙar Ba A Samar da Ayyukan Yi Da Mulki Na Adalci Ba – Amaechi

October 14, 2025
Amnesty International Ta Soki Tinubu Kan Yi Wa Masu Laifin Take Haƙƙin Ɗan Adam Afuwa

Amnesty International Ta Soki Tinubu Kan Yi Wa Masu Laifin Take Haƙƙin Ɗan Adam Afuwa

October 14, 2025
‘Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Jarida A Kan Hanyarsa Ta Zuwa Ɗaukar Horo A Kwara

‘Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Jarida A Kan Hanyarsa Ta Zuwa Ɗaukar Horo A Kwara

October 14, 2025
Zaman Gidan Yari Ya Nuna Min Mutanen Da Ya Kamata Na Yi Hulɗar Siyasa Da Su — Faruk Lawan

Zaman Gidan Yari Ya Nuna Min Mutanen Da Ya Kamata Na Yi Hulɗar Siyasa Da Su — Faruk Lawan

October 14, 2025
Majalisa Na Shirin Sauya Lokacin Zaɓen 2027 Zuwa Nuwamba 2026

Majalisa Na Shirin Sauya Lokacin Zaɓen 2027 Zuwa Nuwamba 2026

October 13, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.