‘Yansanda a jihar Neja sun ceto mutane biyar da aka yi garkuwa da su ciki har da daya da aka yi garkuwa da su daga Sokoto a dajin Neja.
LEADERSHIP ta tattaro cewa, jami’an ‘yansanda da ke a Mararaban Dan-daudu sun ga wani Mubarak Iliya yana gudu cikin dajin, bayan da aka yi masa tambayoyi sai aka fahimci tserewa ya yi daga sansanin ‘yan bindiga wanda daga bisani aka kai shi caji ofishin ‘yansanda na Dibishin Gwada.
- Warware Basussuka: WAEC DA NECO Sun Saki Sakamakon Ɗaliban Zamfara Na Shekara Biyar
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Jami’an Tsaro 5 A Katsina
Hakazalika, wata tawagar jami’an tsaro ta ceto mutane hudu da lamarin ya rutsa da su; Deborah Daina, Gambo Amos, Cyprus Titus, da Satti Iko a karamar hukumar Munya a jihar Neja.
Kakakin rundunar, Wasiu Abiodun, ya ce an yi garkuwa da Ilya ne daga kauyen Gatawa tare da mahaifinsa.
Iliya da mahaifinsa dukkansu daga karamar hukumar Sabon-Birni ta jihar Sokoto. An yi garkuwa da su ne a cikin watan Afrilu, yayin da ‘yan bindigar suka mamaye kauyensu, suna ta harbe-harbe, inda daga nan ne ‘yan bindigar suka yi garkuwa da su Amma Iliya yana zargin an kashe mahaifinsa.
Ilya ya bayyanawa ‘yansanda cewa, ya tsere daga sansanin ‘yan bindigar ne bayan ya yi ta gudu a dajin har na tsawon kwanaki takwas sannan ya hadu da jami’an ‘yansanda a jihar Neja.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp