Dubun wani mutum ta cika bayan da aka cafke shi yana sayar wa mutane garin katako da siminti a matsayin maganin gargajiya.
Wata majiya ta rawaito cewa ‘yansanda sun gano mutumin yana hada garin katako da garin farin simintin inda yake sayar wa mutane a matsayin maganin ciwon zazzabin cizon sauro da sauransu.
- EFCC Ta Gurfanar Da Tsohon Atoni-Janar Na Legas Bisa Laifin Karkatar Da Kudade
- Gwamnatin Tarayya Ta Shiga Tsakani Kan Rikicin Da Ya Kunno Kai Tsakanin Gwamnatin Kogi Da Dangote
A wani bidiyon da aka yi wa mutumin bayan ya shiga hannu, ya ce “Garin katako nake hadawa da garin siminti da kuma garin gypsum da ake yin POP da shi nake kullawa a leda ina sayar wa mutane a matsayin maganin cutar maleriya da sauran cututtuka.
“Ina zuwa kasuwanni daban-daban ina sayarwa kuma mutane suna yawan saya.
“Ba ni da kayyadajjen farashin da nake sayarwa, kawai ya danganta da yadda ciniki ya kaya.
“Na san yana da hatsari, amma saboda yanayin matsayin rayuwar da kasa ke ciki shi ya sa nake yin hakan.”
Wata mata mai suna Taibat, da ke zaune a unguwar Gerewu, ta ce wanda ake zargin yana yawan zuwa kasuwar Mandate da ke Ilori yana sayar da garin, kafin dubunsa ta cika.
Taibat, ta yi kira ga jama’a da su kara lura, sannan ta bukaci gwamnati ta dauki kwararan matakai, inda ta ce Allah ne kadai ya san irin lahanin da garin maganin ya yi wa mutanen da suka yi amfani da shi.
Sai dai kakakin ’yansandan Jihar Kwara, Ajayi Okasanmi, ya ce ba shi da labarin faruwar lamarin.
Amma duk da haka, kakakin ’yansandan ya ce da zarar an sanar da ’yansanda za su dauki mataki.
Idan ba a manta ba a baya-bayan nan hukumar NAFDAC sai da ta yi gargadi kan amfani da wasu magaunguna musamman wanda suke da alaka da gargajiya, inda ta ce suna da hatsari ga lafiyar mutane.