Wata Kotun yanki ta 4 da ke da zama a Yola fadar jihar Adamawa, ta bayar da umarnin tsare wani mutum da aka bayyana sunansa da David Donald a gidan yari, bayan ya amsa laifin da ake tuhumarsa da aikata wa, da kotun ta ce ya saba da sashi na 302 na kundin dokar Nijeriya.
David, wanda ya fito daga karamar hukumar Karim-Lamido ta jihar Taraba, rundunar ‘yan sanda a jihar Adamwa, ta gurfanar da shi a gaban kotun bisa zargin shan giyar burkutu Bokiti 5 da farfesu faranti biyu, ba tare da ya biya ba.
- Tsadar Rayuwa: NLC Ta Shiga Zanga-zanga A Adamawa
- Shirin Yaƙi Da Talauci: Mun Yi Wa Ƙananan Masana’antu 7,000 Rijista A Adamawa – Bawa
Da yake yanke sauraren shari’ar alkalin kotun Ibrahim Musa Ulenda, ya ce mutumin da ake zargin a ranar 21/2/2024, ya ba da umarnin akawo masa burkutu Bokitin roba 5 na robobi da kuma farfesun Kifi faranti 2.
Ya ci gaba da cewa bayan da mutumin ya shanye barasar tare da cin faranti 2 na farfesun kifin a wurin, sai David ya yi kokarin ya gudu, ba tare da ya biya ko kwabo na kudin Giya da farfesun ba, to sai dai bai sa’a ba, nan take aka cika hannu da shi.
Tunda farko da yake gabatar da wanda ake tuhumar, dan sanda mai shigar da kara, Sajen Kabiru Abubakar, ya shaida wa kotun cewa David ya amshi giyar da farfesu na Naira 6,600 daga hannun Felicity Sunday da Linda Ali, bai biya ba, ya nemi ya gudu.
Ya ce mutanen da ya ci da shan kayansu su ka kai kara ofishin ‘yan sanda, inda su ka zargi wanda ake kara da kin biyansu kudi, maimakon haka ya yi yunkurin ya gudu.