ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Abokai Da Ƙawaye Ke Tasiri Wajen Canza Halayen Mutane

by Rabi'at Sidi Bala and Sulaiman
3 weeks ago
Halaye

Shafin TASKIRA shafi ne daya saba zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, ciki sun hadar da zamantakewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya, da dai sauransu. Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da yadda wasu mutanen suke canjawa daga mutanen kirki, masu hakuri da tausayawa, zuwa akasin hakan. Wasu mutanen suna da kirki sosai, da kyawun hali, daga bisani kuma sai a ci karo da su a wasu wuraren tamkar ba su ba, kyawun halinsu da tausayawarsu ya zama tarihi. Musamman idan rayuwarsu ta kara canjawa daga matakin farko zuwa mataki na gaba. Misali; a makarantu, Asibitoci, Kamfanoni da dai sauransu. Wasu na kallon hakan da cewa kawaye ko abokai ne suke canja su, yayin da wasu kuma ke kallon hakan da cewa, daman can halinsu ne hakan waje ne kawai basu samu ba, domin wani baya iya canja wani. Dalilin hakan ya sa shafin TASKIRA jin ta bakin wasu daga cikin mabiya shafin game da wannan batu; “Ko mene ne gaskiyar al’amarin, shin wani ba ya iya canja wani?”

 

Ga dai bayanan nasu kamar haka;

ADVERTISEMENT

Sunana Hafsat Sa’eed, Jihar Neja:

Wasu suna da hakuri juya su kawai ake yi, sai a rika ganin kamar su da kansu suke yi. Musamman a tsarin shugabancin makarantu ko na asibitoci, ko kamfani da sauransu. Wasu dole ake yi musu daga wajen na samansu duk da suna da halin kirki sai a ce sai sun zama marasa kirki (masu zafi) shi ne za su iya kula da waje ko kula dana kasa da su, komai kankantar mukamin da aka basu a wajen. Wasu kuma kawayen da suka hadu da su ne suke ziga su wai kar a raina su, wasu kuma koya suke yi da zarar sun dan taka wani matsayi. Ya kamata mutane su rika aiki da hankali ba wai abin da za a dora su akai mara kyau ba, kai za ka auna da kanka ka ga ya dace ko bai dace ba.

LABARAI MASU NASABA

Me Ya Sa Wasu Maza Ke Gudun Auren Mata ‘Yan Boko Masu Kwarewa Da Wayewa?

Yadda Wasu Iyaye Ke Hana ‘Ya’yansu Auren Matan Da Suka Girme Su Da Zawarawa

 

Sunana Aminu Adamu, Malam Madori, A Jihar Jigawa:

Hakika hakan yana faruwa ka ga mutum ya canja lokaci daya, to amma ba kowa bane wani yake iya canja shi saboda mu’amular yau da kullum sai dai dama idan mutum ba shi da cikakkiyar tarbiyya da kuma ilimin gane abun da ya dace da kuma wanda bai dace ba. To duk mutum mai kyakkyawar dabi’a a cikin al’umma za ka gan shi mutum ne mai tarbiyya, don haka zai yi wuya wani ya canja shi cikin karamin lokaci don haka samun cikakkiyar tarbiyya ita ce hanyar samun kyakkyawar dabi’a.

 

Sunana Hassana Yahaya Iyayi, Jihar Kano:

Gaskiya halayyar jama’a tana canjawa in suka hadu da gurbatattun mutane nan da nan suke saurin dauke dabi’u marasa kyau. Wannan kuma abin dama ba dabi’ace mai kyau ba, Allah ya sa mu dace

 

Sunana Fatima Nura Kila, Jihar Jigawa:

Tabbas Hakan yana faruwa, shi ya sa akodayaushe matukar mutum zai yi abota yayi kokari ya yi da wadda ya fi shi wannnan halin na kirkin da aka san shi, zama yau da kullum shi ne kan janyowa a dauki hali irin na wadancan. Tabbas hakan yakan iya janyo matsaloli a cikin al’umma. Akodayaushe mutum ya rike akidar sa, saboda hakan shi ne ba zai sa ka zama kamar su ba, domin kuwa zama waje daya kuma yau da kullum ta ki wasa.

 

Sunana Lawan Isma’il (Lisary) Rano, A Jihar Kano:

Tabbas zama tare da wasu mutanen sukan canja musu halaye da dabi’u ba wai halinsu ne a haka ba. Misali; za a ga wata matar tana tare da mijinta babu dadin zama har ta kai ga ya auro wata wacce duniya ta yarda ta kirkice, amma idan aka yi rashin sa’a sai uwar gidan ta rinjayeta ita ma ta zama ta banza. Shawarata ita ce mu yi kokari da dadi-babu dadi mu ci gaba da nuna halayenmu na kirki wanda addinimu ya zo mana da shi da kuma wanda aka san malam bahaushe da shi. Ka da mu rika kallon banzan halin da wawayen cikinmu suke aikatawa Allah kasa mu dace amin.

 

Sunana Hassana Sulaiman, Hadejia ,A Jihar Jigawa:

Eh, gaskiyar lamarin hakan na faruwa lokaci zuwa lokaci, za mu iya cewa kasantuwar dabi’a da hali na mutum na sauyawa. Kuma hakan zamu iya cewa na haifar da rashin jituwa tare da raguwar mutanen dake tare da kai duk ta sanadiyyar sauya halin nan naka da kayi tashi guda. Hanyar da ya kamata mutane su himmatu a kanta wajan dawo da dabi’unsu na kirki wanda za ta zama abin kwatance ga sauran mutane ko da bayanan, ya zamana mutum na danne wasu dabi’un nasa a fili, musamman ma marasa kyau da kuma na fushi ga jama’ar da suke kewaye da shi.

 

Sunana Sadi Dauda Baturiya, Kirikasamma, Jihar Jigawa:

Babu shakka akwai mutane da dama da suka canza halayensu daga mai kyau zuwa maras kyau biyo bayan dalilai mabanbanta, ciki kuwa akwai tasirin abokin zama ko tarayya, batun cewa zama da madaukin kanwa ba ya kawo farin kai ba gaskiya bane, domin kuwa ita rayuwa kowa da kaddararsa, abin da ya dace da kowanne dan’Adam dai shi ne ya ji tsoron Allah a duk inda yake kamar yadda Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam ya fada, fatanmu a kullum ya tsaremu daga mummunar kaddara, kuma ya azurtamu da kyakkyawan karshe amin.

 

Sunana Hadiza Ibrahim D. Auta, kaura-Namoda, Jihar Zamfara:

Har kullum Hausawa suna fadin sai hali ya zo daya ake yin abota. Sannan kuma ana yin kamshi idan aka kusanci mai sayar da turare. To kamar haka ne a bangaren hali ko na ce halayya. Sau da yawa mutum zai kasance da halin kirki, amma zama da wani kara-gurbi ya sa shi ma ya koyi wasu abubuwan daga cikin dabi’unsa ba tare da ma ya sani ba. Shi ya sa wasu iyaye masu hikima suke kokarin sanin wane ne abokin dansu, kuma ya ya halayensa suke, idan da matsala suna yin gaggawar yi wa abotar iyaka. Saboda tsoron kusancin nasu ya lalata musu tarbiyyar da suke kokarin ginawa, gudun suna tufka a koma yi musu warawara.

 

Sunana Mohammed Isah, Zareku Miga, A Jihar Jigawa:

Eh a zahiri ana samun irin wadannan mutane da farko ka gansu ba wata matsala, kalau dasu, amma kuma daga baya sai ka ga sun canza. To dama wadansu halinsu ne kawai guri ne basu samu ba. Amma kuma wadannan su abokaine suke canzasu. Matsolilin da hakan ke haifarwa shi ne, rashin kyauwun hali ya kan haifar da rashin tausayin na kasa da kai, taimakon juna da sauran su. Amma kuma idan mutum ya tsinci kansa a irin wannan abokan ya kamata yayi taka-tsam-tsan da kar ya koyi mummunar dabi’a.

 

Sunana Aisha T. Bello, Jihar Kaduna:

Gaskiya in ka ga kana tare da mutun lokaci daya ya canza yana da ra’ayin canza wanne, ko wasu matanen suna bari wasu su yi ‘control’ din rayuwarsu sai abun da suka ce. Shawarata ga masu irin wanan hali shi ne ka da su bawa wani dama ya canza masu rayuwa, idan ma shawara ce suke nema to su nema wajen iyayensu, in kuma ba iyaye Allah na nan shi ne gatan maraya, Allah ya sa mu dace.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Me Ya Sa Wasu Maza Ke Gudun Auren Mata ‘Yan Boko Masu Kwarewa Da Wayewa?
Taskira

Me Ya Sa Wasu Maza Ke Gudun Auren Mata ‘Yan Boko Masu Kwarewa Da Wayewa?

August 31, 2025
Yadda Wasu Iyaye Ke Hana ‘Ya’yansu Auren Matan Da Suka Girme Su Da Zawarawa
Taskira

Yadda Wasu Iyaye Ke Hana ‘Ya’yansu Auren Matan Da Suka Girme Su Da Zawarawa

August 17, 2025
Halaye
Taskira

Natijojin Auren Dattijo Ga Budurwa

July 26, 2025
Next Post
Japanawa Sun Fito Kan Tituna Suna Nuna Fushi Da Katobarar Firaminista Takaichi A Kan Taiwan

Japanawa Sun Fito Kan Tituna Suna Nuna Fushi Da Katobarar Firaminista Takaichi A Kan Taiwan

LABARAI MASU NASABA

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.