‘Yan siyasar kasashen yamma kan karawa batun “rarar kayan da Sin ta samar” gishiri, amma a Afirka, an kira shi “dama ce da ba za ta misaltu ba”. Jaridar South China Morning Post ta Hongkong ta ruwaito kwanan nan cewa, yayin da farashin motocin lantarki na Sin da batir, da wasu sassan kayayyaki ke kara raguwa, kamfanonin Afirka da yawa suna amfani da wannan damar don rage kudin da suke kashewa da samun fasahar da ta dace.
Gupta wanda ya kafa dandalin sufuri mai aiki da lantarki na Afirka na Spiro, ya fada cewa, “Abin da kasashen yamma ke kira ‘rarar kayan da Sin ta samar’, a gare mu, dama ce da ba a iya wasa da ita ba don rage farashin kaya da samun fasaha.”A lokaci guda, kamfanonin Sin suna yiwa tsarin hadin gwiwar sabbin makamashi tsakanin Sin da Afirka kwaskwarima. Daga fitar da motoci cikakke zuwa hada su a Afrika, daga kayan batir zuwa sassan kayayyaki, fasahar Sin da albarkatun Afirka suna kara hadewa da juna cikin sauri. Afirka tana da fiye da rabin ma’adanin kobalt a duniya da kuma albarkatun lithium masu yawa, amma a baya, ta kasance a matakin fitar da danyen albarkatun kasa masu karancin sarrafawa kawai.
Yanzu, jarin da kamfanonin Sin ke zuba na taimakawa Afirka wajen kara karfinsu na sarrafa kayayyaki, matakin da ya dace da bukatun ci gaban Afirka na dogon lokaci, wato ba wai sayar da danyen albarkatu kawai ba, a’a, gina cikakken tsarin masana’antu ne.
Daraktan gudanarwa na asusun yanayi na Afirka, Saliem Fakir, ya ce, “Mutane sun yi tsammanin kasashen yamma ne za su taimaka wajen rage farashin fasahohin samun ci gaba ba tare da gurbatta muhalli ba da samar da isassun kayayyakin da ake bukata a wannan bangare, amma a karshe, Sin ce ta dauki wannan nauyin.” Lokacin da kasashen yamma kamar Amurka da kasashen Turai suka kara haraji kan motoci masu aiki da lantarki na Sin, Afirka ta zabi rungumar damar makamashi mai tsabta da Sin ta samar. Fa’idojin da ake samu sun hada da raguwar farashi da samun fasaha kyauta da kuma kafa cikakken tsarin samar da kaya.
A watan Mayun bana, Sin ta fara aiwatar da manufar soke haraji gaba daya ga kasashe 53 na Afirka da ke da huldar diplomasiyya da ita, a rabin farkon shekara, yawan kayayyakin da Najeriya ta fitar zuwa Sin ya karu da kashi 80%, inda ya kai dala biliyan 2.3. Wannan manufa ta taimaka wa kayayyakin noma na musamman na Afirka da kayan ma’adanai da aka sarrafa su shiga kasuwar Sin cikin sauri, kuma tsarin cinikayya yana karkata zuwa “Hadin gwiwar fasahohi da masana’antu” daga “fitar da danyen albarkatu kawai”.
Lokacin da kasashen yamma suke yada jita-jitar “rarar kayan da Sin ta samar”, Afirka tana cewa “a karshe, dole mu dogara da Sin”. Domin a ganin Afirka, wannan ba matakin sayar da kayayyaki masu yawan gaske cikin farashi mai rahusa ba ne, a’a, dama ce gare mu, wannan ba rara ba ce, a’a, cike gibi ne da ake bukata.
Takardar da ma’aikatar kasuwanci ta Sin ta fitar mai taken “Matsayin Sin game da abin da ake kira ‘rarar kayan da Sin ta samar'” ta bayyana cewa, “Fitar da kayayyaki da yawa da kuma samun ciniki mai yawa ba ya nufin rarar kayayyaki.” Masana’antar motoci masu aiki da lantarki ta Sin ta dogara ne a kan kirkire-kirkire, kuma ta inganta karfin takara dogaro da binciken da take yi a dogon lokaci, a maimakon tallafin gwamnatin.
Lokacin da Amurka da EU suka amfani da matakin haraji kan motoci masu aiki da lantarki na Sin don dakile wannan sana’a, Afirka ta zabi hadin kai da Sin don rungumar damar da ta dace. Saboda abin da Afirka ke bukata ba kariyar kasuwanci ba ne, a’a, saukin samun fasahohi da ci gaba ne. Hadin gwiwar Sin da Afirka ya dace da wadannan bukatun, wato hadin gwiwa da more damammaki da samun ci gaba tare. (Marubuciya:MINA)














